Take a fresh look at your lifestyle.

Jihar Kebbi:Yara Sama Da Sittin Da Shida Na Fama Da Tamowa

Binta Aliyu,Kebbi.

151

A kokarin da Gwamnatin tarayyar Najeriya keyi na inganta kiwon lafiya da Samar da abinci, kididigar ma’aikatan lafiya ta Najeriya na shekara ta dubu biyu da ashirin da takwas ta bayyana cewar jihar Kebbi nada yara Kashi sitin da shida da digo daya, ‘yan kasa da shekaru biyar dake fama da cutar tamowa.

 

Ambrose Evhoesor, jami’in Gamaiyar kungiyoyin farar hula ta Najeriya mai yaki da rashin abinci mai- gina jiki ga yara wato civil society scaling up Nutrition in Nigeria” CS- SUNN” shine ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki akan lafiyar yara, Wanda aka gudanar a Birnin Kebbi.

 

Ambrose Evhoesor, ya Kara da cewa, dole Gwamnatoci su tashi tsaye domin yaki da wannan cutar ta “Tamowa” ganin irin i’lolin dake yiwa kananan yara, Wanda ya shafi rashin girma da rashin ilimi a kwakwalwa tun suna kanana.

 

Ambrose Evhoesor jami’in “CS- SUNN” yace, akallah jihohi goma sha- tara daga cikin Talatin da shidda a Nijeriya suka aiwatar da wannan Shirin na abinci mai- gina giki ga yara.

 

Mai- baiwa Gwamna Jihar kebbi, shawara akan- gudunmawar aiyokan lafiya Dakta Usman Buhari Aliyu yace, wannan sabuwar Gwamnati tana kokarin ganin ta Samar da ingantacen lafiya ga Al’umma.

 

Dakta Usman Buhari Aliyu ya Kara da cewar Gwamnatin jihar tana kokarin ganin ta fitar da abinci domin rabawa ga al’ummar jihar kyauta.

 

 

Binta Aliyu.

Comments are closed.