Take a fresh look at your lifestyle.

Alamun Barkewar Cutar Shan Inna A Jihar Kebbi Arewa Maso Yammacin- Najeriya

Binta Aliyu,Kebbi.

95

An samu rahotanni na alamun barkewar cutar shan- Inna wato Polio a kananan hukumomi tara daga cikin ashirin da biyar a Jihar Kebbi.

 

Babban jami’in wayar da kan- jamaa a ma’aikatar kiwon- lafiya matakin farko Yusuf Umar Sauwa shine ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki a jihar.

 

Yusuf Umar Sauwa, babban yace tuni gwamnatin jihar ta tura kwararu domin gudanar da aiyyukan bincike da zai tantance irin barnar da wannan cutar tayi domin fito da sabbin hanyoyin magance ta.

 

Yusuf Umar Sauwa, ya bayyana Kananan hukumomin da cutar ta shafa har da Argungu da Augie da Suru da Bagudo da Gwandu da Aliero da Fakai da Danko- Wasagu da kuma Birnin Kebbi babban birnin Jihar.

 

A ranar talatin da daya ga watan Janairun wannan shekara, Gwamnatin Tarayyar Najeriya tare da hadin guiwar Gidauniyar GAVI da kuma Asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) suka gina katafaren cibiyar agajin gaggawa tare da kayayyakin aiki da kuma motocin Hilux Uku donin aiyyukan  magance Shan Inna a Jihar Kebbi.

 

Babban Daraktan Asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya UNICEF a Nijeriya, Christiana Munduate tace Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohi hudu a Nijeriya dake da alamun wannan cutar ta Polio.

 

 

Binta Aliyu.

Comments are closed.