Wani hari da jiragen yakin kasar Isra’ila suka kai kan wani gini da ke gundumar Kafr Sousa a birnin Damaskus na kasar Sham a ranar Larabar da ta gabata, ya kashe mutane biyu, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin Sham ta sanar.
Wata majiyar soji da gidan talabijin na gwamnatin Sham ya rawaito ta ce harin da aka kai da misalin karfe 9:40 na safe (0740 GMT) ya raunata wasu da dama, inda aka bayyana wadanda suka mutu a matsayin farar hula.
Hotunan da kafafen yada labaran gwamnatin Siriya suka wallafa sun nuna gefen wani bene mai bene da ya kone. Majiyar tsaron ta ce “harin bai cimma manufar shi ba”.
Babu dai wani karin haske daga rundunar sojin Isra’ila.
REUTERS/Ladan Nasidi.