Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Najeriya Ya Gana Da Yakubu Gowon

127

A halin yanzu, shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu yana ganawa da tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), a fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.

 

Wannan shi ne ganawarsu ta farko tun bayan da shugaba Tinubu ya hau mulki a watan Mayun bara.

Ba a bayyana dalilin taron ba ga manema labarai.

 

Gowon tsohon shugaban sojan Najeriya ne mai ritaya wanda ya rike mukamin shugaban kasa daga 1966 zuwa 1975.

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.