Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Yayi Alkawarin Farfado Da Tattalin Arziki, Ya Samar Da Kwamitin Ba Da Shawara

145

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bada tabbacin cewa farfado da tattalin arziki na nan tafe yayin da yake kaddamar da kwamitin ba da shawara ga shugaban kasa kan tattalin arziki da zai magance kalubalen tattalin arziki, samar da abinci, da tsaron kasa.

 

A wata ganawa da ya yi da shugabannin masana’antu da manyan ‘yan kasuwan Najeriya, da kuma wasu ‘yan kungiyar gwamnonin Najeriya a fadar gwamnati da yammacin jiya Lahadi a Abuja, shugaba Tinubu ya bayyana damuwarsa kan jin dadin ‘yan Nijeriya tare da dora wa shugabannin ‘yan kasuwar aikin su hada hannu da gwamnati tare da kawo sauye-sauye ga tattalin arzikin Najeriya.

 

A yayin da yake jaddada mahimmancin yi wa jama’a hidima, shugaba Tinubu ya yi kira da a gudanar da tantance kai na kasa domin gano tare da daidaita manufofin da ke kawo cikas ga farfado da tattalin arzikin kasar.

A cewarsa, “Bari mu kalli abin da muke yi daidai da abin da muke yi ba daidai ba don dawo da rayuwa cikin tattalin arziki. Kamar yadda na sha fada a lokuta da dama, al’ummar kasar nan ne kawai mutanen da ya kamata mu farantawa. Kuma mun damu sosai tun daga dalibai zuwa uwa uba, manoma, ’yan kasuwa, mu gane cewa kowane dayanmu zai debo ruwa a rijiya daya.

 

“Muna neman karin kokarin da ka iya taimakawa ‘yan Najeriya da ke fama da talauci kuma za mu ba da wannan fata da kuma tabbatar da cewa farfadowar tattalin arziki yana kan hanyarsa,” in ji Shugaba Tinubu.

Shugaban na Najeriya ya amince da sarkakiyar kalubalen da ke fuskantar al’ummar kasar; don haka ya jaddada kudirin gwamnati na magance su.

 

Shugaba Tinubu ya kara bayyana shirye-shiryen Marshall Plan a matsayin wani muhimmin bangare na dabarun tattalin arzikin gwamnatinsa.

 

“Ba muna cewa muna da dukkan amsoshi ba. Amma ba za a zarge mu da rashin ƙoƙari ba. Muna tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za mu yi iya bakin kokarinmu don ganin mun samar da shirin mu na farko da kuma fitar da mafi kyawun makomar tattalin arzikin kasar nan,” in ji shugaban.

 

Tattaunawar Taro

 

Da yake magana a kan sakamakon taron, shugaban gidauniyar Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa tattaunawar tasu ta fi mayar da hankali ne kan tattalin arziki, samar da abinci da kuma tsaron kasa.

 

Dangote ya bayyana cewa, sabon kwamitin ba da shawara ga shugaban kasa da aka kafa zai yi cikakken bayani kan batutuwa daban-daban da suka hada da samar da ayyukan yi da samar da abinci.

 

“Ina ganin mun yi taro mai kyau sosai kuma abin da muka tattauna gaba daya ya shafi tattalin arziki, samar da abinci da kuma tsaron kasa. Mun tattauna komai dalla-dalla. Sannan akwai kwamitin ba shugaban kasa shawara kan tattalin arziki, wanda aka kafa. Ina ganin wannan zai duba dukkan batutuwan da magance su, daga samar da ayyukan yi, samar da abinci, da tattalin arziki.

 

Ya bayyana fatansa cewa kwamitin na da duk wani abu da zai iya kawo wa tattalin arzikin Najeriya garambawul, ta yadda za a sake dawo da martabar kasar.

 

“Amma muna da bege kuma mu al’umma ce mai girma. Muna da abin da ake bukata don juya tattalin arziki kuma za mu yi hakan.

 

Shima da yake jawabi a wajen taron, shugaban kamfanin simintin na BUA, Abdulsamad Robiu, ya bayyana cewa taron ya tattauna muhimman batutuwa da suka hada da hauhawar farashin canji da kalubalen da ake fuskanta a watannin baya.

 

Robiu ya kara da cewa, taron ya yi nazari kan hanyoyin da za a bi wajen dakile karuwar kudaden musaya na kasashen waje, tare da sanin yadda ake yin amfani da fasahar kere-kere da yadda ake gudanar da kasuwancin FX a halin yanzu a Najeriya.

 

“Abu a bude yake, gaskiya ne, kuma ya cika. Sannan wasu daga cikin batutuwan da muka tattauna, alal misali, batun kudin kasar waje, wanda muka san shi ne matsalar tun watanni biyu ko uku da suka gabata. Mun tattauna a kan yadda za a rage darajar kudin kasashen waje domin duk mun san cewa abin da ke faruwa dangane da canjin kudi ne na wucin gadi, yin magudi ne kuma alhamdulillahi CBN yana yin abubuwa da yawa. Yanzu dai farashin canji ya ragu daga N1800 zuwa wata kila 1600 da 1500, kuma kamar yadda kuka sani komai na Najeriya ana lissafinsa ne da kudin kasashen waje, musamman idan ana maganar kayayyakin da muke shigo da su kasar nan.”

 

Shugaban gidauniyar Tony Elumelu, Mista Tony Elumelu, ya ce taron da shugaban Najeriyar ya kira ya ciyar da tattalin arzikin Najeriya gaba, sannan ya taimaka wajen kawar da talauci, samar da ayyukan yi, da samar da wadataccen abinci ga ‘yan Najeriya.

 

“Na bar wannan taron ne da nishadi, farin ciki da kuma kyakkyawan fata game da makomar kasarmu. Na yi imanin cewa aiwatar da shawarar da muka cimma a yau zai inganta tattalin arzikinmu da kuma taimakawa wajen rage radadin talauci a cikin ƙasa, taimakawa wajen samar da ayyukan yi da kuma taimakawa wajen sanya abinci a kan tebur.

 

Darakta-Janar na kungiyar masu masana’antu ta Najeriya, Mista Segun Ajayi-Kadir, ya ce kamfanoni masu zaman kansu na fatan aiwatar da shawarwarin da aka cimma da shugaban kasa, sannan kuma masana’antun a Najeriya suna fatan samun kyakkyawan yanayin kasuwanci.

 

Ajayi-Kadir ya ce an tattauna batutuwan da suka shafi canjin kudaden waje, rashin tsaro da kuma yanayin kasuwanci a Najeriya gaba daya a wajen taron kuma sabon kwamitin da aka kafa ya samu tabbacin shugaba Tinubu kan gagarumin sauyi a tattalin arzikin Najeriya.

 

“Don haka ina ganin kamfanoni masu zaman kansu suna sa ran aiwatar da mafi yawan shawarwarin da muka yi da shugaban kasa. Masu kera suna sa ido ga yanayin da zai dace da kasuwanci. Don haka ne aka tattauna batutuwan da suka shafi canjin kasashen waje, rashin tsaro da yanayin aiki gaba daya. Mun samu tabbacin daga Maigirma Shugaban kasa nan ba da jimawa ba za mu fara ganin wasu manyan sauye-sauye. Ina ganin kwamitin ba da shawara da aka kafa, kamfanoni masu zaman kansu za su taka rawar gani sosai. ‘Yan Najeriya, ya kamata a ci gaba da fatan cewa muna samun mafita ga kalubalen da muke da su,” in ji Kadir.

 

Mambobin kwamitin sun hada da Aliko Dangote, Femi Otedola, Abdulsamad Robiu, Amina Maina, Boye Olusanya, SegunAjayi Kadir, Tony Elumelu, Bismarck Rewane, Samala Zubairu, Innocent Chukwumah, Kola Adeshina, Gwamna Dapo Abiodun, Gwamna Charles Soludo, Jubril Adewale.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.