Take a fresh look at your lifestyle.

An Kashe ‘Yan Kasashen Waje A Hadarin Mota A Tanzaniya

136

‘Yan kasashen waje na kasashe bakwai na daga cikin mutane 25 da suka mutu a wani hadarin mota da ya rutsa da motoci hudu a kan babbar hanyar zuwa birnin Arusha na arewacin Tanzaniya.

 

Hadarin dai ya faru ne a lokacin da wata babbar mota kirar kasar Kenya ta abkawa wasu motoci guda uku ciki har da daya dauke da ‘yan kasashen waje masu aikin sa kai a wata makaranta.

 

Mata 10, maza 14 da mace daya ne suka mutu a hatsarin na ranar Asabar, kamar yadda fadar shugaban kasar ta fitar a ranar Lahadi.

 

Akalla mutane 21 da suka hada da na wasu kasashe ne suka jikkata a hadarin.

 

Wadanda suka mutu sun hada da wani Ba’amurke, da dan Afirka ta Kudu da wasu ‘yan kasar Kenya da Togo da Madagascar da kuma Burkina Faso.

 

Sanarwar ta kara da cewa wadanda suka jikkata sun fito ne daga kasashen Najeriya, Ivory Coast, Kamaru, Switzerland, Birtaniya da kuma Mali.

 

‘Yan sanda na neman direban babbar motar da ya yi hatsarin, wanda aka ce ya gudu bayan faruwar lamarin.

 

Shugabar kasar Samia Hassan ta mika ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka mutu tare da yin kira ga masu ababen hawa da su bi ka’idojin kiyaye hanya.

 

 

 

BBC/Ladan Nasidi.

Comments are closed.