Take a fresh look at your lifestyle.

Sabon Shugaban Kasar Kenya Yayi Aderishin Yan Majalisu

175

Shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya yi jawabi a taron hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar, inda mambobin majalisar dattijai da na majalisar dokokin kasar suka yi taro domin gabatar da jawabi.

Shugaban majalisar dokokin kasar Moses Wetangula da takwaransa na majalisar dattawa Amason Kingi sun bayyana cewa jawabin shugaban kasar ya bi sashe na 132 (1) (a) na kundin tsarin mulkin kasar da ya bukaci shugaban kasa ya yi jawabi a bude kowace sabuwar majalisar da aka zaba.

Shugaban ya zayyana manufofi da muhimman abubuwan da suka sa a gaba a tsarin tattalin arziki na kasa wanda ya yi yakin neman zabe a kai wanda gwamnatinsa za ta nema ta cimma.

An rantsar da majalisar ta 13 ne a ranar 8 ga watan Satumba bayan kammala babban zaben da aka gudanar a ranar 9 ga watan Agusta.

Zauren na zuwa ne a daidai lokacin da ake gwabza kazamin fada tsakanin shugaba Ruto da abokin hamayyarsa, tsohon firaminista Raila Odinga, yayin da dukkaninsu ke ikirarin samun rinjaye a majalisar dokokin kasar.

labaran africa

Comments are closed.