An bayar da rahoton mutuwar mutane biyu a wani hatsarin jirgin sama, wanda ya hada da wani jirgin horo da wani jirgin fasinja a Nairobi babban birnin kasar Kenya, kamar yadda ‘yan sandan yankin suka sanar a ranar Talata.
Sanarwar da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kenya ta fitar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1005 a tsakanin wani jirgin sama mallakar wata makaranta mai tashi da jirgin saman fasinja na Safarilink.
Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida Safarilink ya ce fasinjojin da ke cikin jirginsa da ke kan hanyarsa ta zuwa wurin shakatawar Diani da ke gabar teku ba su samu rauni ba.
“Zan iya tabbatar da wani dalibi da mai horarwa (a cikin jirgin horo) sun mutu a lokacin da lamarin ya faru,” kwamandan ‘yan sandan gundumar Nairobi Adamson Bungei ya ruwaito ba tare da bayar da karin bayani ba.
Reuters/Ladan Nasidi.