Take a fresh look at your lifestyle.

Harin Barkaram: Manyan Tawagar Najeriya Sun Gana Da Shugaban Kasar Chadi Déby

74

Shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno, ya karbi bakuncin tawagar Najeriya karkashin jagorancin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, bayan harin ta’addanci da aka kai a tsibirin Barkaram, wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin kasar da dama.

 

Tawagar ta hada da babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, Manjo Janar Emmanuel Undiandeye, shugaban hukumar leken asiri ta tsaro, Manjo Janar Ali Salau, kwamandan rundunar MNJTF da sauran manyan jami’an tsaro.

 

Tawagar ta isar da rubutaccen sako daga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zuwa ga shugaba Deby.

A cikin sakon, shugaba Tinubu ya bayyana jajenshi da goyon bayanshi ga shugaban kasar Chadi da al’ummar kasar sakamakon harin ta’addanci da aka kai kwanan nan.

Taron dai ya kara jaddada alaka mai karfi da ke tsakanin Chadi da Najeriya, musamman wajen tinkarar kalubalen tsaro a yankin da kuma yaki da ta’addanci.

Kasashen biyu dai sun dukufa wajen karfafa hadin gwiwarsu domin inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tafkin Chadi.

 

 

Ladan Nasidi

Comments are closed.