Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wa majalisar dokokin kasar wasika, yana neman amincewar Naira tiriliyan 1.77, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.209 a matsayin sabon shirin karbo bashi daga waje a cikin dokar kasa ta 2024.
Bukatar shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman majalisar a ranar Talata.
Shugaba Tinubu ya ce rancen zai kasance wani bangare ne na kudaden da za a yi amfani da su wajen kashe Naira tiriliyan 28.7 na shekarar 2024.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa bukatar shi ta kasance daidai da tanadin sashe na 21 (1) da na 27 (1) na ofishin kula da basussuka da kuma amincewar majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).
“A bisa tanadin sashe na 21 (1) da na 27 (1) Ofishin Gudanarwa na Jiha, DMO ta kafa Dokar a 2003 da amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya, na rubuta bukatar neman kuduri na Majalisar Dokoki ta kasa domin tara jimillar $2.206 da aka bayar a matsayin sabon rance na waje a cikin Dokar Haɓakawa ta 2024, ” kamar yadda wasikar ta kumsa.
Sai dai shugaban majalisar dattawa, Sanata Akpabio ya mika bukatar ga kwamitin majalisar dattijai mai kula da basussukan cikin gida da waje sannan ya umurci ‘yan majalisar da su kai rahoton binciken su ga majalisar dattawa cikin sa’o’i 24.
Ladan Nasidi.