Uwargidan shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu, ta bayyana rashin amincewarta da duk wani nau’i na cin zarafin mata a cikin kasar.
A jawabinta na bikin cika kwanaki 16 na fafutukar kawar da cin zarafin mata, Misis Tinubu ta jaddada muhimmancin hada kai wajen kare hakkin mata.
“A yau, na bi sahun al’ummar duniya wajen bikin tunawa da ranar kawar da cin zarafin mata ta duniya, wanda ke nuna farkon kwanaki 16 na fafutukar yaki da cin zarafin mata.
“Cin zarafin da ya danganci jinsi ya kasance daya daga cikin cin zarafin bil’adama mafi yaduwa, inda kusan daya daga cikin mata uku a duniya ke fuskantar cin zarafi ta jiki ko ta jima’i a rayuwarsu,” in ji uwargidan shugaban kasar.
Misis Tinubu ta ce dole ne a kawar da munanan ayyuka kamar auren yara da kuma kaciya, domin a ba da cikakken ‘yancin ‘yan mata da mata.
“A Najeriya, har yanzu munanan ayyuka masu cutarwa kamar auren kananan yara da kuma kaciyar mata, wanda galibi ana yin su ta hanyar al’ada ko addini.
“Duk da cewa muna samun ci gaba mai ban mamaki, amma, mata da ‘yan mata da yawa, musamman a yankunan karkara da marasa galihu, sun kasance cikin tarko a cikin wadannan tashe-tashen hankula da rashin daidaito.
“Dole ne mu dauki matakin hadin gwiwa a dukkan bangarori na al’umma. Ba da rahoto da gurfanar da masu laifi a kan lokaci, ƙarin tallafi ga waɗanda abin ya shafa da waɗanda suka tsira suna da mahimmanci domin samar da yanayi mafi aminci ga mata da ‘yan mata,” in ji ta.
Uwargidan shugaban kasar ta bukaci mata da su rika kalubalantar munanan ayyuka tare da fallasa masu cin zarafin mata.
Ta ce: “Yayin da muke kiyaye wadannan kwanaki 16 na fafutuka, ina rokon mu da mu karbe wannan lokacin a matsayin kira ga kowannenmu don kalubalantar halaye masu cutarwa.
“A gare ni, karatun boko ga yarinyar ya kasance mabuɗin ’yantar da su da kuma taimaka musu su zaɓi zaɓi na gaskiya.
“Bari mu yi aiki tare don tabbatar da al’umma mafi aminci inda kowa, ba tare da la’akari da jinsi ba, zai iya rayuwa ba tare da tsoron tashin hankali ba.”
Ladan Nasidi.