Take a fresh look at your lifestyle.

An Yaba Wa Gwamnan Jihar kano Saboda Ya Samar Da Kayayyakin Karatu

331

An yaba wa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf bisa samar da tebura da kujeru 73,800 ga makarantu a jihar kuma wannan mataki ya yi matukar rage wa dalibai wahalar zama a kasa domin daukar darasi .

 

Da yake yabon a ranar Litinin , shugaban makarantar Yelwa Model dake karamar hukumar Dala,Umar Aliyu, a lokacin da yake zantawa da tawagar ‘yan jarida, ya kara da cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba ta wannan hanyar.

 

Ya kara da cewa “Dole ne mu yi wa gwamnatin jihar godiya saboda ta sanya dokar ta baci kan ilimi, duk da cewa makarantar  ba ta amfana da wannan karimcin ba.”

 

Sai dai Mallam Aliyu ya zayyana wasu kalubalen da makarantar ke fuskanta, inda ya ce makarantar tana da dalibai 1,164 da malamai 36 ciki har da shi kansa amma babu bandaki masu anfani.

 

Baya ga haka, babu katanga mai da aka kewaye makarantar, wannan ya ce ya bai wa barayin damar cikin sauki wajen sace dukiyar makarantu ba tare da kama su ba.

 

A cewar shi an yi sata a makarantar inda aka sace kayayyaki da dama a cikin watanni biyun da suka gabata.

 

“Kamar yadda kuke gani katangar makarantar ta yi gajarta sosai kuma hakan ya sa makarantar ta yi kaca-kaca ta hanyar ba masu laifi damar shiga harabar.

 

“Kamar yadda kuke gani Barayi sun huda rufin ofishina, da kuma ofishin na’ura mai kwakwalwa inda suka sace wayoyin wutar lantarki .

 

“Sun kuma sace injin janareta na makaranta da tukunyar iskar gas na firjin mu na Samsung da injin rijiyoyin burtsatse da kudinsu ya kai N500,000.”

 

Sai dai a lokacin da suke zantawa da manema labarai Shugan dalibai maza da ta dalibai mata Saminu Sanusi da Khadija Ahmed , sun yi kira ga gwamnatin jihar ta samar wa makarantar da isassun bandakuna.

 

Sai dai Shugaban makarantar firamare ta Ungogo special da ke Ungogo, Haladu Tanko, ya jaddada bukatar gwamnatin jiha ta magance rashin isassun malamai a makarantar.

 

A cewar shi, “Da jimillar dalibai 2,943, malamai 15 ne kawai suka suke koyar da dimbin daliban makarantar.

 

Ya kuma bayyana cewa abin da ya fi muni shi ne, babu bandakuna masu aiki, lamarin da ke haifar da babbar illa ga lafiyar yara.

 

Ya kuma kara da cewa babu wata ma’aikatar kula da lafiya, lura da cewa daliban da suka kamu da rashin lafiya ana kai su Asibiti  da ke kusa.

 

“Ba mu da bandaki mai aiki a makarantar, ba mu da gidan wanka, amma muna da rijiyar burtsatse, duk da cewa ta lalace, amma har yanzu ana iya gyarawa,” in ji shi.

 

Shugaban dalibai maz makarantar, Nura Yusuf da Shugabar dalibai mata, Jamila Isah Suleiman , sun kuma tabbatar da halin bakin ciki na rashin bayan gida da daliban suka yi, inda suka yi kira ga gwamnati da ta gina musu bandaki tare da samar musu da kwararrun malamai.

 

Sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar da bandakunan da bai gaza goma ba wanda hudu kowannen su zai raba yayin da sauran biyun za su kasance na malamansu.

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.