Take a fresh look at your lifestyle.

FG, Ta Kulla Yarjejeniya Da Jihar Adamawa Domin Haɓaka Ayyukan Lafiya

376

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kulla yarjejeniya da gwamnatin jihar Adamawa domin inganta harkokin kiwon lafiya ta hanyar mayar da Asibitocin karkara dake Hong da babban asibitin Mubi zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya.

 

Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, wanda babban sakataren ma’aikatar, Daju Kachollom (mni) ya wakilta, ya bayyana yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) a matsayin wani muhimmin mataki na daidaitawa da kudirin gwamnatin tarayya na fadadawa da samun ingantacciyar kiwon lafiya a karkashin tsarin sabunta bege na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

 

Bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ya nuna wani gagarumin ci gaba na  ayyukan kiwon lafiya a jihar Adamawa da yankin Arewa maso Gabas.

 

“Wannan yunƙurin yana da mahimmanci domin haɓaka isar da lafiya, ba kawai ga Mubi da Hong ba har ma da Arewa maso Gabas da ƙasashe makwabta,” in ji Farfesa Pate.

 

Ya nanata cewa sauya wadannan wuraren zuwa Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Tarayya an tsara shi ne domin daukaka matsayin kiwon lafiya da kuma tabbatar da ingantacciyar isar da aiyyuka.

 

Mataimakin gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Kaletapwa Farauta, wanda ya jagoranci taron, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa hangen nesa da take bi wajen karfafa fannin kiwon lafiya a jihar.

Ta bayyana cewa shirin ya yi daidai da manufofin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na inganta harkokin kiwon lafiya a fadin jihar.

 

“Gwamnatin jihar ta ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa wadannan cibiyoyi domin tabbatar da nasarar su,” in ji Farfesa Farauta.

 

Kwamishinan lafiya da ayyukan jin kai na jihar, Cif Felix Tangwami, ya kuma nuna godiya ga ma’aikatar lafiya da jin dadin jama’a ta tarayya bisa kokarin da take yi na inganta harkar kiwon lafiya a jihar Adamawa.

 

Yarjejeniyar na nuna babban manufar Gwamnatin Tarayya na inganta kayayyakin kiwon lafiya a fadin kasar, tare da inganta cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya da ake sa ran za su zama wata fitilar ƙwararrun likitoci a yankin.

 

“Wannan haɗin gwiwar an tsara shi ne domin kawo gagarumin alfanu ga al’ummar jihar Adamawa da ma fiye da haka, domin inganta hanyoyin samar da ayyukan kiwon lafiya na zamani da kuma ciyar da tsarin kiwon lafiyar al’umma gaba.”

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.