Take a fresh look at your lifestyle.

Rashin Aikin yi: Gwamnatin Najeriya Za Ta Samar Da Ma’aikata Miliyan 12

130

Gwamnatin tarayyar Najeriya zata gwiwa da shirin samar da ayyukan yi ga matasa manoma miliyan goma sha biyu da kuma masu sana’ar abinci da shirin bunkasa tattalin arzikin matasa na Najeriya NIYEEDEP.

 

Wannan shiri dai na nufin yaki da rashin aikin yi da talauci a tsakanin matasa tare da magance matsalolin da suka shafi tauyewa da rashin tsaro.

 

Ministan, Ma’aikatar Raya Matasa ta Tarayya, Kwamared Ayodele Olawande, ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a lokacin da ya karbi bakuncin NIYEEDEP, karkashin jagorancin jami’in hada shirye-shirye, Kennedy Iyere, a ofishin shi da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

 

Kwamared Olawande ya bayyana cewa shirin zai samarwa matasan Najeriya tsarin tattalin arziki da damammaki da ake bukata domin su zama masu kirkiro ayyukan su da kuma sauya kan su zuwa masu kawo canji ,ci gaban kasa, samar da arziki, kawar da fatara da aikata laifuka, sauyin zamantakewa da ci gaban tattalin arziki.

 

Ministan ya bayyana cewa, “Shirin zai mayar da hankali ne kan wasu dabarun hada-hadar tattalin arziki kamar, Shirin hadin gwiwar Matasan Manoma.”

 

Karanta kuma: Gwamnati Ta Koyawa Matasa 541 Sana’o’in Aikin Noma Na Zamani Domin Yakar Rashin Aikin Yi

 

Ya bayyana cewa ana son cimma wannan shiri ne ta hanyar kirkirowa da gudanar da kungiyoyin kasuwanci na kasa da na hadin gwiwa, hada hannu da sa hannun jari mai inganci da kuma shigar da matasa sana’o’in noma da abinci.

 

“Haɗin gwiwar zai taimaka wajen haifar da juyin juya hali na samar da wadata, a cikin muhimman sassan tattalin arziki kamar fasaha, nishaɗi, makamashi mai sabuntawa, kasuwancin dijital, kirkire-kirkire da kere-kere da sauran su tare da manufar samar da ayyukan yi miliyan 6 da ƙari,” in ji shi.

 

Kwamared Kennedy Iyere, kodinetan hukumar NIYEEDEP, ya bayyana matukar godiyar shi ga ministan bisa namijin kokarin da yake yi na inganta ayyukan da suke bunkasa tattalin arziki.

 

Ya kuma tabbatar wa da ministan kudirin shi na aiwatar da shirin yadda ya kamata, tare da jaddada karfin shi na bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da kuma bunkasa ci gaban al’umma gaba daya.

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.