Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kashe Naira Miliyan 739 wajen Tallafama Wadanda Matsalar Tsaro Ta Shafa.
Kamilu Lawal, Katsina.
Gwamnatin jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya ta kashe naira miliyan Dari Bakwai Da Talatin Da Hudu Da Naira Dubu Dari Ukku Da Naira Dari Biyar Da Arba’in Da Daya (739,330,541) wajen Aiwatar da shirye shirye da dama na tallafawa wadanda matsalar Ta’addanci ta shafi rayuwarsu.
Daga cikin wadanda aka tallafawa akwai iyalan mutum 1136 da kuma mutum 1640 wadanda aka biya ma kudin magani a asibitoci daban daban sakamakon raunuka iri iri da suka samu.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Katsina, Sa’idu Ibrahim Danja a wani taron manema labarai da ya kira a birnin Katsina.
Sa’idu Danja ya bayyana cewa daga cikin kudin anyi amfani da naira Military 151 wajen kula da lafiyar wadanda suka samu raunuka sakamakon hare haren yan bindigar, yana mai cewa “taimakon ba yana nufin biyan diyya ne ga iftila’in da ya same su ba, illa dai wani tsari ne da gwamnatin jihar ta bullo dashi domin ragema wadanda matsalar tsaron ta shafa radadin abinda ya same su.
Ya ce gwamnatin ta kuma fadada irin wannan taimako zuwa ga iyalan jami’an tsaron da suka rasa rayukansu wajen arangama da yan ta’addan dajin.
Mai taimakama gwamnan ya kara da cewa duk a cikin tsare tsaren ne gwamnatin take kai daukin kayan abinci ga wadanda hare haren suka shafa a yankunan jihar.
Ya yabama gwamnan jihar, Malam Dikko Radda bisa tausayin sa na tallafama wadanda lamarin ya shafa a daidai lokacin da kuma gwamnatin sa ta dukufa wajen murkushe yan ta’addan a duk inda suke a fadin jihar.
Kazalika, ya yaba wa kungiyoyin kasa da kasa bisa tallafin da suke baiwa jihar Katsina wajen ganin ta magance kalubalen tsaro a jihar.
Kamilu Lawal.