Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya taya zababben shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama murnar nasarar da ya samu a babban zaben kasar Ghana da ya gudana a ranar 7 ga watan Disamba, biyo bayan jawabin amincewa da abokin hamayyar shi ya yi.
A wata tattaunawa da ya yi da Mahama ta wayar tarho, Shugaba Tinubu ya ce yana fatan hawan Mahama a karagar mulki a karo na biyu zai kara samar da zaman lafiya a kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), wadda shugaba Tinubu ne shugaban ta.
Shugaba Tinubu ya yaba wa ‘yan kasar Ghana bisa jajircewarsu wajen tabbatar da dimokuradiyya, wanda ya ce an nuna shi ta hanyar gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki cikin lumana da nasara.
Shugaban na Najeriya ya kara bayyana shirin yin aiki tare da gwamnatin shugaba Mahama mai jiran gado domin karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu a sassa daban daban da kuma samar da makoma mai haske a yankin yammacin Afirka.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mista Bayo Onanuga ya fitar ta bayyana cewa, shugaban na Najeriya ya kuma yaba wa ‘yan kasar Ghana kan yadda suka sake nunawa duniya cewa dimokuradiyya ita ce hanyar da aka fi so wajen samun kwanciyar hankali ta fuskar siyasa, ci gaban tattalin arziki, adalci ga al’umma, da gudanar da mulki cikin gaskiya a Afirka.
Ya tabbatar da cewa akidar Najeriya da kuma ka’idojin yankin na ‘yancin jama’a na zaben shugabanninsu cikin ’yanci zai kasance abin alfahari.
Shugaban na Najeriya ya yaba wa dan takarar jam’iyyar New Patriotic Party (NPP), mataimakin shugaban kasar Ghana, Dr Mahamudu Bawumia, saboda amincewa da shan kaye kafin hukumar zaben Ghana ta bayyana a hukumance.
Shugaba Tinubu ya ce matsayin Bawumia ya karfafa tsarin dimokradiyyar Ghana.
Shugaba Tinubu ya yi nuni da cewa, komawar zababben shugaban kasa Mahama gidan Jubilee, bayan ya rike mukamin shugaban kasa daga shekarar 2012 zuwa 2017, ya nuna yadda al’ummar Ghana suka amince da shugabancin shi da kuma tunanin shi na kai kasar zuwa ga tudun mun tsira.
Mahama ya rike mukamin mataimakin shugaban kasar Ghana daga shekarar 2009 zuwa 2012, dan majalisar wakilai daga 1997 zuwa 2009, ya kuma rike mukamai na mataimakin shi da minista tsakanin 1998 zuwa 2001.
Shugaba Tinubu ya sake sabunta cikakken goyon bayan shi na zurfafa dankon zumunci tsakanin Najeriya da Ghana, kamar yadda tarihi, alakar al’adu, goyon bayan juna da hadin gwiwa, manufofin kasashen Afirka, dimokuradiyya, bin doka da oda, da hada-hadar tattalin arziki.
Shugaban na Najeriya ya kuma godewa shugaba Nana Akufo-Addo saboda kyakkyawan jagoranci da kuma gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Ghana da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ladan Nasidi.