Katsina; NOA Ta Kaddamar Da Gangamin Wayar Da Kan Al’ummar Najeriya Kan Wasu Mahimman Batutuwa
Kamilu Lawal, Katsina
Ofishin Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta kasa dake jihar Katsina arewa maso yammacin Najeriya NOA,ya kaddamar da wani gangamin wayar kan al’umma kan muhimman wasu batutuwa guda biyar da ke ciwa al’ummar Najeriya tuwo a kwarya
Taron kaddamar da wadannan abubuwa guda biyar muhimmai sun hadar da walwalar al’umma da hadin kai da samar da cigaba ya gudana ne a dakin taro na sakatariyar gwamnatin tarayya dake birnin Katsina..
Taken taron shine “Wayar da kan al’umma kan muhimmancin bin ka’idoji da samar da cigaba ga kasa.” wanda ke da burin ganin an samar da hadin kai a tsakanin ‘yan Najeriya don tunkarar kalubale da ke damun kasa.
Da yake jawabi ga taron manema labaran, babban daraktan hukumar ta NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu da ya samu wakilcin daraktan shari’a a hukumar, Mista Williams Dogo ya ce hukumar zata mayar da hankali kan muhimman abubuwa guda biyar.
“Gangamin zai mayar da hankali kan abubuwa biyar.
“Ranar yaki da cutar HIV ta Duniya da wayar da kan al’umma kan batun tsaro da fadakar da al’umma kan su guji kokarin ganin sun yi kudi cikin hanzari, ranar kare hakkin bil Adama ta duniya da kudirin dokar haraji.”
Ranar cutar HIV ta Duniya: Gwamnati ta kara kokari wajen bada magunguna kyauta da yin gwaji da ba da shawarwari a fadin kasa.
“Ya kamata al’umma su rungumi wadannan damarmaki da aka bayar domin inganta harkokin kula da lafiya.”
“Wayar da kai kan tsaro: Gwamnati na inganta harkokin tsaro ta hanyar samar da kayan aiki da horo da Karin kudade ga cibiyoyin tsaro.
“Ana karfafa ma al’umma gwiwa su ba da rahoton duk wani abu da suka ga alamun zargi, sannan su hada kai da jami’an tsaro.”
“Al’umma su gujema akidar son samun dare daya”: Gwamnati na kokarin samar da ayyukan yi ga matasa da daukar hukunci ayyukan zamba cikin aminci.”
“Ana karfafa gwiwar al’umma su guji dabi’ar son yin arziki dare daya su rungumi dabi’ar dattako da aiki tukuru da kokarin amfanuwa da duk wasu damarmaki da gwamnati ta bullo dasu domin yan kasa su samu arziki halastacce.”
Kudirin dokar haraji:
“Gwamnati na aiwatar da gyara a kudirin dokar haraji ta yadda za a samu sassauci wanda a cewar jami’in na NOA kamata yayi al’umma su mayar da hankali su sami ilimi kan manufar wannan kudiri da abinda ya kunsa kasancewar akwai kwararru da ke nuni da cewa akwai tarin alfanu da ke tattare da kudirin wanda al’umma ya kamata su sani kuma NOA za ta yi duk mai yiwuwa a wannan fanni”.
Taron manema labaran ya samu halartar wakillan kafafen yada labarai daban daban wadanda suka hada da na gwamnati da masu zaman kansu.
Darektan ofishin hukumar wayar da kan al’umma ta kasa a jihar Katsina, Muntari Lawal Tsagem ya bayyana cewa wayar da kan al’ummar kasa wajibi ne domin cigaban kasa
Yace kowace kasa zata iya cigaba ne kadai idan al’umarta suka fahimci manufofin da ta sanya a gaba domin cigabansu kuma suka bada gudummuwarsu wajen samun nasarar aiwatar da su
A lokacin taron kaddamar da gangamin yan jaridar sun gudanar da tambayoyi domin samun karin bayani akan ayyukan hukumar NOA wajen kokarin wayar da kan al’ummar Najeriya domin samun nasarar gangamin.
Kamilu Lawal.