Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Burkina Faso Ya Nada Sabon Firaminista

132

Kwana guda bayan rusa gwamnati ba tare da wani bayani ba, gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta nada Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo a matsayin sabon Firaministan kasar.

 

Sanarwar ta fito ne ta hanyar dokar shugaban kasa Ibrahim Traore ya karanta.

 

Ouedraogo, dan jarida kuma makusancin Traore, ya taba rike mukamin ministan sadarwa da kuma kakakin tsohuwar gwamnatin.

 

Ya kuma rike manyan mukamai a gidan rediyon jihar, ciki har da babban edita da darakta.

 

Ba a bayar da wani dalili na korar Apollinaire Joachim Kelem de Tambela, wanda ya rike mukamin Firaministan rikon kwarya tun watan Satumban 2022, jim kadan bayan Traore ya kwace mulki a wani juyin mulki.

 

Burkina Faso dai ta fuskanci rudanin siyasa a ‘yan shekarun nan, inda gwamnatin mulkin Traore ta kori Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda a baya ya jagoranci juyin mulkin da aka yi na tsige zababben shugaban kasar Roch Marc Kaboré.

 

Kasar dai na daya daga cikin kasashen yammacin Afirka da dama da sojoji suka mamaye, sakamakon rashin jin dadin jama’a da gazawar gwamnatocin farar hula wajen magance matsalolin tsaro da ke kara tabarbarewa.

 

Duk da alkawarin dawo da kwanciyar hankali da gwamnatin mulkin sojan kasar ta yi, Burkina Faso na ci gaba da kokawa da karuwar hare-haren ta’addanci.

 

Wadannan hare-haren sun kashe dubban mutane tare da raba sama da mutane miliyan biyu da muhallan su,da kananan yara.

 

Manazarta sun yi kiyasin cewa kusan rabin yankunan kasar ya rage a hannun gwamnati.

 

Gwamnatin rikon kwarya ta Burkina Faso tana aiki ne a karkashin kundin tsarin mulkin da majalisar dokokin kasar ta amince da shi wanda ya kunshi hafsoshin soja, kungiyoyin farar hula, da shugabannin gargajiya da na addini.

 

Da farko dai, gwamnatin mulkin sojan ta yi alkawarin gudanar da zabukan dimokuradiyya nan da watan Yulin shekarar 2024 a karkashin matsin lamba daga kungiyar ECOWAS.

 

Sai dai a watan Mayu, ta tsawaita wa’adin mika mulki da shekaru biyar na tsawon wa’adin shugaban kasa.

 

Baya ga Nijar da Mali da su ma suka fuskanci juyin mulki, Burkina Faso ta yanke hulda da kawayenta na Yamma da kungiyoyin shiyya, ciki har da kungiyar ECOWAS, wadda kasashen uku suka fice a farkon wannan shekarar baki daya.

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Comments are closed.