Take a fresh look at your lifestyle.

Muhimmancin Muhawara Kan Gyaran Haraji Ga Mulkin Dimokuradiyya – Ministan Yada Labarai

204

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya ce muhawarar da jama’a ke ci gaba da yi a kan kudirin gyaran haraji, abu ne mai matukar muhimmanci a tsarin mulkin dimokuradiyya, saboda tsara manufofi da muhawara ba zasu rabu ba.

 

Idris ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin Cibiyar Progressive Institute karkashin jagorancin Darakta Janar, Lanre Adebayo, a wata ziyarar ban girma da suka kai ofishin shi, a Abuja.

 

Ministan ya bayyana cewa, kyakkyawar hulda da masu ruwa da tsaki da jama’a kan duk wata manufa ta gwamnati zai tabbatar da cewa manufofin sun yi daidai da bukatu da muradun ‘yan kasa.

“Bari mu dauki tsarin gyara haraji misali, wanda ya haifar da mahawara da yawa inda wasu ke cewa muhawarar ta sabawa manufofin gwamnati ko kuma shugaban kasa . Ina tsammanin waɗannan muhawarar lafiya ce da dukanmu muke yi don mu inganta wannan lissafin. Ga duk wanda ke tunanin cewa muhawara da fitar da manufofin sun bambanta da juna, ina ganin hakan ba daidai ba ne.

 

“A koyaushe za ‘a sami damar yin muhawara mai kyau ta yadda duk abin da gwamnati za ta sa gaba, za a iya inganta shi. Ko ta yaya, ana yin hakan ne domin amfanin dukkan ‘yan Nijeriya. Saboda  haka ’yan Najeriya na da ‘yancin yin tambayoyi ga manufofin gwamnati, idan har sharhohin sun kasance cikin koshin lafiya kuma sun dace da inganta manufofin,” inji shi.

 

Ya kuma jaddada cewa sake fasalin Harajin da Shugaban Kasa ya gabatar, ba wai an yi shi ne ya sanya wani bangare na kasar nan cikin wani hali ba, a’a, an tsara shi ne domin inganta ci gaban da ya hada da bunkasa harkokin tattalin arziki a fadin kasar nan, kamar yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawari da zai samar da ci gaba mai ma’ana da wadata ga dukkan ‘yan Najeriya.

 

Hakazalika Ministan, ya karfafa gwiwar ‘yan Nijeriya da su taka rawar gani wajen tattaunawa kan manufofin gwamnati, domin gudunmuwar da suke bayarwa na da matukar amfani wajen karfafa tsarin dimokuradiyyar kasa.

Gyare-gyaren da shugaban kasa ya kafa na jajircewa da ake ganin suna da tsauri amma hanya mafi inganci ne don cika alkawarin da ya dauka a yakin neman zabe na samar da ci gaba da wadata ga daukacin ‘yan Najeriya.

 

“Sauyin yawanci yana da wahala, amma da zarar an bi su, za su ba da sakamako mai ban mamaki kuma mun san cewa alkiblar da wannan gwamnati za ta bi, muna da kwarin guiwar cewa duk matakan gyare-gyaren da shugaban kasa ya kafa za su kai mu zuwa inda ake so,” inji shi.

 

Idris ya bayyana jin dadin shi da cewa kawo yanzu ‘yan Najeriya sun fara ganin alfanun sauye-sauyen, musamman ta hanyar kyawawan alkaluma na baya bayan nan da hukumar kididdiga ta kasa ta bayar kan ayyukan tattalin arziki.

 

Ya yaba wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, bisa kafa cibiyar cigaba, inda ya bayyana cewa an yi niyya ta zama dakin injinin jam’iyyar da kuma gwamnati ta hanyar bincike kan manufofi da shirye-shiryen da gwamnati za ta aiwatar.

 

Tun da farko Darakta Janar na Cibiyar Progressives, Lanre Adebayo, ya bayyana cewa, a karon farko a tarihin jam’iyyun siyasa a Najeriya, jam’iyyar APC ta shagaltu da cibiyar ta zama wata kungiya mai tunani tare da samar da ginshikin basira don inganta iya aiki, daukar jagoranci da bincike kan manufofin gudanarwa.

 

Ya bukaci goyon bayan Ministan domin taron da cibiyar ke shiryawa kan koyon sana’o’i, kasuwanci da kalubalen ci gaba a kasar nan.

 

Adebayo ya yaba wa Ministan bisa dabarun da ya bi wajen sadar da manufofi da tsare-tsare na gwamnatin Shugaba Tinubu, yace ba fada ko mayar da martini ba ne.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.