Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban VON Ya Yaba Wa Minista Kan Ayyukan Al’umma A Jihar Neja

920

Darakta Janar na Muryar Najeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace, ya yaba wa ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris bisa aikin raya kasa da ya aiwara a mahaifar shi Malagi.

 

Malam Ndace ya yi wannan yabon ne a lokacin kaddamar da ayyuka daban-daban da Ministan ya aiwatar, da nufin tallafa wa al’ummar Malagi a karamar hukumar Gbako da ke Jihar Neja a Arewa ta Tsakiya Najeriya.

Ya bayyana ayyukan da suka hada da masallacin da ya dace, makarantar Islamiyya, rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana, da gyaran makarantar firamare a matsayin gagarumin nasarori.

 

DG VON ya bayyana cewa, shirye-shiryen da ministan ya yi sun nuna halin bayar da gudummawa ga al’umma, musamman ga al’ummar kakannin shi, kuma zai inganta rayuwar mazaunan ta.

 

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa al’umma za su ci gaba da amfana daga ayyukan raya kasa masu ma’ana da “dan kasa” ke jagoranta.

 

Malam Ndace, wanda ke cikin tawagar ministan a yayin bikin kaddamarwar, ya yabawa al’ummar Malagi bisa karramawar da suka yi da kuma hadin kai wajen karbar dimbin maziyartan da suka halarci taron.

Ya kuma bukaci al’umma da su tabbatar da an yi amfani da su yadda ya kamata tare da kula da ayyukan a kai a kai, inda ya ce ministan na da shirye-shiryen kara kawo wasu tsare-tsare masu fa’ida ta fuskar tattalin arziki kai tsaye ga al’umma da jihar Neja baki daya.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.