Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya isa birnin Maiduguri na jihar Borno a wata ziyara.
Mataimakin shugaban kasar yana jihar shi ne domin hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.
Ya sauka a filin jirgin saman Muhammad Buhari da misalin karfe 15:16 agogon GMT.
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum da wasu mambobin majalisar zartarwa ta jihar Borno sun tarbi mataimakin shugaban kasar.
Karanta kuma: Kirsimeti: Shugaba Tinubu ya taya Kiristoci murna
Yayin da yake jihar, ana sa ran zai gana da abokan shi na siyasa da dangin shi.
Ladan Nasidi.