Jagoran Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Amurka bisa rasuwar tsohon shugaban kasar Jimmy Carter.
Carter ya mutu yana da shekaru 100.
Shugaba Tinubu a wata sanarwa da mai magana da yawun shi, Mista Bayo Onanuga ya fitar, ya kira shugaba Carter a matsayin amintaccen kuma mai tausayin Najeriya.
Ya yaba da irin gudunmawar da marigayi Carter ya bayar ta hanyar Cibiyar Carter, musamman kokarin shi na kawar da cutar kurkunu da kuma makanta a koguna a Najeriya, wadanda suka inganta rayuwar ‘yan Najeriya da dama.
Shugaba Tinubu ya ce; “Marigayi Carter ya tunkari kalubalen da kasashe masu tasowa ke fuskanta, daga yaki da cututtuka zuwa sasanta rikice-rikice da inganta dabi’un demokradiyya. Ya misalta alheri, daraja, da kuma matuƙar girmamawa ga ɗan adam.”
Dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka, Shugaba Tinubu ya tuna da ziyarar tarihi da Carter ya kai Najeriya a watan Maris 1978 da kuma zaman shi na kwanaki uku a gidan gwamnati da ke Marina, jihar Legas.
“A karkashin jagorancin Carter, wannan ziyarar ta nuna wani muhimmin lokaci a manufofin ketare na Amurka. Ya aza harsashin kulla kyakkyawar alaka tsakanin Amurka da Afirka, tare da Najeriya a zuciyarta.
Shugaban na Najeriya ya ci gaba da cewa, Carter ya nuna wa duniya yadda za a ci gaba da kasancewa masu dacewa da tasiri bayan ya bar mukamin shugaban kasar Amurka.
Carter, Shugaban Amurka na 39, ya kasance fitilar hidima ga bil’adama, yana nuna wa shugabannin duniya babban tasirin sadaukarwa fiye da mafi girman ofishi.
Shugaba Tinubu ya ce; “A matsayin shi na wanda ya lashe lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel kuma ɗan jahohin duniya, Shugaba Carter ya sadaukar da rayuwar shi bayan shugabancin shi ga abubuwan da ke haifar da zaman lafiya, dimokuradiyya, da kuma kawar da cututtuka masu zafi. Jajircewar shi na ci gaba da gudanar da ayyukan shi masu daraja ya bar wani tarihi da ba zai gushe ba a duniya.
Ya bayyana fatan cewa abin da Carter ya gada na ladabi, hali, da mutuntaka, a ciki da waje, zai ci gaba da zaburar da Amurkawa da shugabanni a duk duniya don su rungumi ainihin jagoranci.
Cibiyar Carter ta tabbatar da cewa tsohon shugaban kasar Amurka, Jimmy Carter ya rasu yana da shekaru 100 a duniya, a ranar Lahadi da yamma a gidan shi da ke Plains, Georgia.
Ya ce; “Carter ya shiga kulawar asibiti a watan Fabrairun 2023, yana zabar zama a gida bayan gajeriyar zaman asibiti. A shekara ta 2015 ne dai aka tabbatar da cewa tsohon shugaban ya kamu da cutar daji. Yana da shekaru 100, shi ne shugaban kasar Amurka mafi dadewa.
Jam’iyyar Democrat ce ta shugabanci Amurka daga 1977 zuwa 1981.
Ladan Nasidi.