Shugaba Tinubu Ya Daukaka Matsayin Cibiyoyin Gargajiya A Hadin Kan Kasa
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba da rawar da hukumomin gargajiya ke takawa wajen samar da hadin kan kasa, bunkasar tattalin arziki da shugabanci a matakai daban-daban.
Da yake jawabi bayan karbar bakuncin Mai Martaba Sarkin Ijebuland, Awujale na Ijebuland, Oba Sikiru Kayode Adetona, Ogbagba II, a gidansa da ke Legas a Ikoyi, Jihar Legas, shugaban ya jaddada aniyar gwamnatin shi na karfafa hadin gwiwa da shugabannin gargajiya.
“Yanzu fiye da kowane lokaci, rawar da cibiyoyin mu na gargajiya ke da mahimmanci don samar da haɗin kan kasa, mulki, da ci gaban tattalin arziki a matakai daban-daban,” in ji Shugaba Tinubu a wata sanarwa da aka raba a shafinsa na X.
Shugaban ya bayyana dangantakar shi da Awujale a matsayin mai amfani, yana mai da hankali kan samar da ingantattun hanyoyin magance kalubalen Najeriya.
Tattaunawar ta yi nuni da bukatar samar da hadin kai na kasa baki daya da ke goyan bayan kyawawan dabi’u tare da samar da ci gaba da wadata ga ‘yan kasa.
Har ila yau Karanta: Shugaban Kasa Tinubu Ya Aminta Da Kamfanoni A Matsayin Mabudin Ci Gaba
Da yake bayyana kyakkyawan fata, Shugaba Tinubu ya lura cewa irin wannan haɗin gwiwar na da mahimmanci don cimma burin gwamnatinsa na samun ƙarfi, haɗin kai, da wadata Najeriya.
“Mun tattauna hanyoyin magance kalubalen Najeriya, inda muka jaddada bukatar kulla kawance da samar da kyakkyawar kasa.
“Wannan asalin ya kamata ya ƙunshi kimarmu a matsayinmu na al’umma tare da samar da ci gaba da wadata ga dukkan ‘yan ƙasa.
“Wannan kyakkyawar alaka da Kabiyesi ta bani kwarin gwuiwa yayin da gwamnatinmu ke ci gaba da yin aiki tukuru domin samun ingantacciyar Najeriya mai karfi, wadata da hadin kai,” in ji Shugaba Tinibu.
Ladan Nasidi.