Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Taya Da Jaridun THISDAY Cika Shekaru 30 Da Kafuwa

1,417

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya kamfanin jaridar THISDAY da gudanarwa da ma’aikatan ta murnar cika shekaru 30 da kafuwa.

 

A cikin wata sanarwar taya murna da kakakin shugaban kasar Mista Bayo Onanuga ya fitar shugaban ya yaba wa mahukuntan wannan gidan jarida bisa jajircewar da suka yi na tabbatar da akidar kasuwanci ta ‘yanci dimokuradiyya da amfani da fasahar kere-kere da kuma bunkasa sunaye da dama a harkar yada labarai.

 

Shugaba Tinubu ya kuma bayyana cewa yawan lambobin yabo da jaridar ta samu da editocinta da mawallafanta suka samu tsawon shekaru wata shaida ce da ta nuna kwazon jaridar.

 

Shugaba Tinubu ya yi fatan Jaridun NAN za su ci gaba da bunkasa a shekaru masu zuwa.

 

An kafa kungiyar ne a ranar 22 ga Janairu 1995 wanda Yarima Nduka Obaigbena ne ya kafa kungiyar ta kafafen yada labarai kuma ta yi fice a matsayin jarida mai tarihi a Najeriya inda ta gabatar da zurfafa labaran abubuwan da ke faruwa a kasa da duniya.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.