Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta jaddada aniyar ta na ci gaba da gudanar da ayyukanta na shari’a bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan umarnin kakabawa ma’aikatanta takunkumi.
Kotun ta ICC ta ce tana tsayawa tsayin daka da jami’anta kuma za ta ci gaba da samar da “adalci da fata” ta kara da cewa umarnin na neman cutar da aikinta na “mai zaman kansa da rashin son kai”.
Umarnin na Trump ya zarge shi da “ayyukan da ba su dace ba kuma marasa tushe da suka shafi Amurka da kuma aminiyarmu ta Isra’ila”.
“Kotu ta tsaya tsayin daka da jami’anta kuma ta yi alkawarin ci gaba da samar da adalci da bege ga miliyoyin wadanda ba su ji ba ba su gani ba a duk fadin duniya a duk yanayin da ke gabanta.”
Takunkumin ya sanya takunkumin kudi da biza kan daidaikun mutane da iyalansu wadanda ke taimakawa a binciken ICC na ‘yan Amurka ko abokan kawance.
Alkalai a kotun sun ce akwai dalilai masu ma’ana cewa Netanyahu tsohon ministan tsaronsa Yoav Gallant da Mohammed Deif na Hamas suna da alhakin laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.
BBC/Ladan Nasidi.