Take a fresh look at your lifestyle.

Mutane Shida Sun Mutu Daga Wuta A Kasar Koriya Ta Kudu

157

Mutane 6 ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani otel da ke birnin Busan mai tashar jiragen ruwa na kasar Koriya ta Kudu a cewar hukumar kashe gobara ta birnin tare da wani jirgin sama mai saukar ungulu ya kwaso wasu mutane 14 domin tsira bayan da suka fake a saman rufin.

 

Kimanin mutane 100 ne aka kwashe a wurin da ake aikin gine-ginen, inda ake ci gaba da gudanar da ayyuka a gine-gine uku masu hawa 12 sama da kasa uku in ji hedkwatar wuta da bala’i ta Busan.

 

Wani jami’in hukumar kashe gobara ta Busan ya fada a gidan talabijin kai tsaye cewa mutane kusan 25 ne suka samu raunuka ciki har da wasu sakamakon shakar hayaki.

 

Hukumar kashe gobara ta ce da alama gobarar ta tashi ne a cikin kayan kariya da aka loda a kusa da wani wurin shakatawa na cikin gida da ke hawa na farko na daya daga cikin ginin.

 

Mukaddashin shugaban kasar Koriya ta Kudu Choi Sang-mok ya ba da umarnin a yi amfani da dukkan albarkatun da ake da su wajen kashe gobarar, in ji ofishin shi a cikin wata sanarwa.

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Comments are closed.