Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Jihar Osun Ya Rantsar Da Sabbin Kansilolin Da Aka Zaba

59

Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun a kudu maso yammacin Najeriya ya rantsar da shugabannin kananan hukumomi 30 da aka zaba a zaben kansiloli da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a jihar.

 

Gwamna Adeleke yayin da yake rantsar da su a fadar gwamnati da ke Oke-fia Osogbo babban birnin jihar ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin lamari.

 

“Da godiya ga Allah da mutanen jihar Osun nagari da masu kaunar dimokuradiyya na yi muku maraba da zuwa wannan gagarumin biki. Mun zo nan ne don kammala tsarin dimokuradiyya wanda dukkanmu muka yi aiki tukuru don cimmawa” inji shi.

 

Gwamnan wanda ya tuno da tsarin zaben kananan hukumomi ya bayyana cewa hukumar zabe ta jihar OSSIEC ta bi duk wasu dokokin da suka dace wajen gudanar da zaben.

 

Ya bayyana cewa fitowar shugabannin ya biyo bayan tsarin da ya dace kuma ya samo asali ne daga dokokin kasar.

 

“Dukkanmu muna sane da tafiya zuwa inda muke. A yau ne jihar ke gudanar da aikin da aka fara shekara daya ko fiye da haka. Hukumar zaben jihar ta fitar da sanarwar da ya dace na zaben shekara guda da ta gabata.

 

Adeleke ya ce “Na san hukumar ta bi duk wasu ka’idoji da tsare-tsare wadanda suka kai ga samar da sabbin shugabannin kananan hukumomi da kansiloli” in ji Adeleke.

 

Bada fifikon shugabanci na gari

 

A yayin da yake taya sabbin zababbun shugabannin kungiyar murnar wannan aiki nasu Gwamnan ya umarce su da su ba da fifiko wajen gudanar da shugabanci nagari ta hanyar samar da tsare-tsare masu inganci wadanda suka dace da tsarin jam’iyyar PDP domin amfanin al’umma.

 

Ya kuma umarce su da su kasance masu kawo canji a tsarin gwamnatinsa ta hanyar sauya wuraren da suke da tasiri ga mafi kyau.

 

Ya ce “Ina ba ku umarni da ku samar da tsare-tsare a cikin kundin tsarin jam’iyyar PDP. A yayin da gwamnatinmu ke kawo sauyi ga jihar nan ina kira gare ku da ku zama wakilan canji masu ci gaban al’umma da samar da ribar dimokuradiyya.”

 

Daga nan sai Gwamna Adeleke ya yabawa shugaba Tinubu kan kasancewarsa mai bin tafarkin dimokuradiyya tare da tabbatar masa da kudirin gwamnatinsa na tabbatar da bin doka da oda da kundin tsarin mulki ta fuskar mulki da warware rikici.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.