Gwamnatin Jigawa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta shekaru biyu da kungiyar Medecins San Frontiers (MSF), domin yaki da mace-macen mata masu juna biyu a jihar.
KU KARANTA KUMA: MSF na kula da yara 46,304 da ke fama da tamowa a Kano
kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu Mista Sagir Musa shine ya bayyana hakan a karshen taron majalisar zartarwa ta jiha (SEC) ranar Talata a Dutse.
Ya ce yarjejeniyar za ta karfafa aikin dakile mace-macen mata masu juna biyu da jarirai ta hanyar samar da ingantacciyar kula da masu juna biyu a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na Jahun da Aujara da Miga.
Musa ya ce majalisar ta amince da Naira biliyan 1.5 domin biyan diyya ga masu filayen da ayyukan titunan gari ya shafa a fadin jihar.
Ya lissafa hanyoyin da suka hada da Fagam da Kila zuwa Jugwa zuwa Sakuwa zuwa Gwaram da Sankara zuwa Ringim da Bulangu zuwa Kafin Hausa da Gandun Sarki zuwa Hadejia da Dansure zuwa Roni da Aujara zuwa Jahun da Dutse.
Kwamishinan ya ce SEC ta kuma amince da Naira biliyan 8.3 don biyan kashi 30 cikin 100 na kayan aikin noman shinkafa gabaɗaya a lokacin noman rani na 2025.
“Wannan shine don inganta wadatar abinci da rayuwa ga miliyoyin ‘yan kasa ta hanyar baiwa manoma dubu hamsin da takwas da dari biyar rance don noma hekta dubu hamsin na shinkafa a gungu 1,000 a fadin yankunan da ake noman shinkafa a jihar.
“Manufar karfafa kokarin gwamnati don ganin jihar Jigawa ta samu nasara wajen noman shinkafa a kasar nan” in ji shi.
NAN/Ladan Nasidi.