Take a fresh look at your lifestyle.

Zelenskiy Ya Nufi Saudiyya Gabanin Tattaunawar Da Amurka

90

Shugaba Volodymyr Zelenskiy ya tafi Saudiyya don ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a yau litinin gabanin tattaunawa tsakanin jami’an Ukraine da na Amurka kan kawo karshen yakin da Rasha a wani lokaci mai cike da fargaba ga Kyiv.

 

Amurka, wacce a da ita ce babbar kawar Ukraine, ta inganta manufofinta na lokacin yakin a kokarinta na ganin an kawo karshen fada cikin gaggawa tare da yin hulda da Moscow kai tsaye yayin da ta katse taimakon soji da musayar bayanan sirri ga Kyiv.   Ana sa ran Zelenskiy zai gana da yarima mai jiran gado na Saudiyya wanda kasar shi ta taka rawar shiga tsakani daban-daban tun bayan mamayar kasar Rasha a shekarar 2022 ciki har da musayar fursunoni da karbar bakuncin tattaunawa tsakanin Rasha da Amurka a watan jiya.  

 

Tattaunawar ta ranar Talata tsakanin jami’an Amurka da na Ukraine ganawa ta farko a hukumance tun bayan wata mummunar arangama da ofishin Oval ya yi tsakanin Zelenskiy da shugaban Amurka Donald Trump ana sa ran za ta mai da hankali kan yarjejeniyar ma’adinai da kuma yadda za a kawo karshen yakin.   A karkashin babban matsin lamba daga Trump wanda ke son kawo karshen yakin da sauri Zelenskiy ya sha wahala don nuna cewa suna kan hanya ɗaya duk da rashin samun tabbacin tsaron Amurka da Kyiv ke ganin yana da mahimmanci ga duk wata yarjejeniyar zaman lafiya.

 

Zelenskiy ya ce ba zai halarci tattaunawar ta ranar Talata da jami’an Amurka ba kuma tawagar ta Yukren za ta hada da babban hafsan hafsoshin shi da ministocin shi na harkokin waje da na tsaro da kuma wani babban jami’in soji a gwamnatin shugaban kasar.   “A gefenmu muna da cikakkiyar himma ga tattaunawa mai ma’ana kuma muna fatan tattaunawa da amincewa kan yanke shawara da matakan da suka dace” in ji Zelenskiy a cikin wani sakon shi na X.  

 

“Shawarwari na gaskiya suna kan tebur. Makullin shine tafiya cikin sauri da inganci.”   Jami’an Amurka sun ce suna shirin yin amfani da ganawar da ‘yan Yukren a wani bangare don sanin ko Kyiv na son yin rangwame ga Rasha don kawo karshen yakin.   “Ba za ku iya cewa ‘Ina son zaman lafiya ba kuma Na ƙi yin sulhu a kan komai” in ji ɗaya daga cikin jami’an game da tattaunawar da za a yi.

 

Tsarin Yarjejeniyar

 

Wakilin Trump na musamman Steve Witkoff wanda ke shirya tattaunawar ya ce manufar ita ce “saukar da tsarin yarjejeniyar zaman lafiya da kuma tsagaita bude wuta na farko”.

 

Zelenskiy ya yi kira da a tsagaita wuta ta sama da teku da kuma yin musayar fursunoni a wani abu da ya ce ka iya zama wani gwaji na matakin da Rasha ta dauka na kawo karshen yakin.   Masko ta yi watsi da ra’ayin tsagaita wuta na wucin gadi wanda shi ma Birtaniya da Faransa suka gabatar da shi yana mai cewa wani yunkuri ne na bai wa Kyiv lokaci da kuma hana rugujewar sojojin ta.

 

Zelenskiy ya kuma ce Kyiv a shirye yake ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ma’adinai da Amurka wanda zai samar da wani asusu na hadin gwiwa daga sayar da ma’adinan Yukren. Washington ta ce yana da matukar muhimmanci a ci gaba da samun goyon bayan Amurka.  

 

Reuters/Ladan Nasidi.

Comments are closed.