Take a fresh look at your lifestyle.

Kakakin Majalisar Jihar Nasarawa Yayi Kira Ga Ba Mata Akan Gina Kasa

207

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Dokta Danladi Jatau ya yi kira ga matan Nijeriya da su ci gaba da bayar da gudunmawar da ta dace wajen ci gaban kasa.

 

Jatau, wanda ke wakiltar mazabar Kokona ta Yamma ya yi wannan kiran ne a taron shekara-shekara na kungiyar al’adu da ci gaban Eggon (ECDA) bagaren Mata ranar Lahadi a karamar hukumar Nassarawa Eggon.

 

Taron yana da taken “Bikin Shekaru 25 na Hidimar Al’umma na Makarantar Firamare ta Eggon Kyenkyen Nassarawa Eggon”.

 

Shirin dai an yi shi ne don tara kudade don ci gaban makarantar.

 

Jatau ya ce mata na taka rawar gani wajen ci gaban kowace al’umma.

 

Ya yabawa reshen mata na ECDA kan taron shekara-shekara da kuma inganta al’adun Eggon ya kuma bukace su da kada su yi kasa a gwiwa.

 

“Ina rokon ku da ku ci gaba da inganta al’adunku don samar da zaman lafiya da hadin kai” in ji shi.

 

Kakakin majalisar ya kuma bukaci sauran ‘yan jihar da su ci gaba da nuna kauna da rayuwa cikin hadin kai da zaman lafiya domin ci gaban jihar baki daya.

 

Ya umarce su da su ci gaba da addu’a tare da marawa gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule baya domin samun nasara.

 

Daga bisani Jatau ya bayar da tallafin Naira miliyan daya a matsayin tallafi na ci gaban kungiyar da kuma makarantar.

 

Tun da farko shugabar kungiyar ECDA Women Wing Misis Rose Attah ta ce an shirya taron ne domin inganta hadin kai da zaman lafiya a tsakanin mambobin kungiyar.

 

Ta ce haka kuma an yi bikin cika shekaru 25 na makarantar Eggon Kyenkyen Primary School Nassarawa Eggon tare da tara kudade domin ci gaban makarantar.

 

 

NAN/Ladan Nasidi.

Comments are closed.