Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango Felix Tshisekedi ya gana da dan majalisar dokokin Amurka Ronny Jackson inda suka tattauna batun yaki a gabashin kasar da kuma damar da Amurka za ta samu na saka hannun jari in ji fadar shugaban kasar Congo.
Taron ya gudana mako guda bayan da Washington ta ce a shirye ta ke ta binciko muhimman alakar ma’adanai da Kongo. Wani dan majalisar dokokin Kongo a watan Fabrairu ya tuntubi jami’an Amurka don kulla wata yarjejeniya ta ma’adinai don tsaro.
Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta bayyana Jackson a matsayin “Congo” ga shugaban Amurka Donald Trump.
Tshisekedi dai na fuskantar tada kayar baya daga ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda a gabashin Kongo kuma gwamnatinsa na shirin aikewa da tawaga zuwa tattaunawar zaman lafiya a Angola ranar Talata.
Kongo tana da dumbin tanadi na cobalt da lithium da uranium da sauran ma’adanai.
Gwamnati ba ta fito fili dalla-dalla game da shawarar kulla yarjejeniya da Amurka ba tana mai cewa tana neman hadin gwiwa iri-iri.
Reuters/Ladan Nasidi.