Take a fresh look at your lifestyle.

Kotun Tunusiya Ta Yanke Wa Shugabannin ‘Yan Adawa Hukuncin Dauri

79

A ranar Juma’ar da ta gabata ne kasar Tunisiya ta yanke hukuncin dauri a gidan yari ga fitattun ‘yan adawar kasar Kais Saied inda ta same su da laifin shirya zagon kasa ga tsaron kasar.

 

Issam Chebbi da Jawhar Ben Mbarek shugabannin jam’iyyar adawa ta National Salvation Front tare da lauya Ridha Belhaj da mai fafutuka Chaima Issa, an yanke musu hukuncin daurin shekaru 18 a gidan yari a cewar lauyansu.

 

An yanke wa dan kasuwa Kamel Eltaief hukuncin daurin shekaru 66 a gidan yari.

 

Suna cikin mutane 40 da suka hada da manyan ‘yan siyasa ‘yan kasuwa, da ‘yan jarida wadanda ake tuhumar su da laifukan tsaro da ta’addanci.

 

Masu sukar sun yi zargin cewa tuhume-tuhumen na da nasaba da siyasa kuma wani bangare ne na kamfen din kara karfin ikon Saied.

 

A shekarar da ta gabata ne dai aka sake zaben shugaba Saied ba tare da hamayya ba bayan daure ko kuma haramtawa abokan hamayyar takara a karkashin abin da masu lura da al’amuran yau da kullum suka bayyana a matsayin rashin gaskiya.

 

Tun bayan rusa majalisar dokoki a shekarar 2022 Saied ya fi yin hukunci da doka. A cikin 2023 ya kafa tsarin mulkin da aka yi wa kwaskwarima wanda ya kara fadada ikon shugaban kasa sosai.

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Comments are closed.