Tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan, ya ce bambancin al’adu yana kawo zaman lafiya da hadin kai a tsakanin kungiyoyin da’a daban-daban a fadin duniya.
Ya bayyana hakan ne, a yayin ziyarar ban girma da mai martaba Ooni na Ife, mai martaba Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ọjájá II, ya kai masa a gidansa dake Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, a kudancin Najeriya.
Ziyararsa ta sarauta da goyon bayansa na alheri na nuna dawwaman na hadin kai da mutunta juna, a tsakanin al’ummarmu, abin tunatarwa mai karfi, muhimmancin hakuri da zaman lafiya a tsakanin kabilu daban-daban na Najeriya.
Ya ci gaba da bayyana cewa, “ya yi matukar farin ciki da karbar bakuncin Ooni na Ife, ya kuma mika godiyarsa ga Ooni da mukarrabansa bisa wannan ziyara da aka kawo masa, da kuma kyaututtukan sarauta, wadanda ke da gaskiya da dimbin al’adunmu”.
Aisha.Yahaya, Lagos