Take a fresh look at your lifestyle.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi Ta Tsare Wasu Jami’anta Uku Bisa Zarginsu

49

Runduna ‘Yan sanda Jihar Kebbi Ta jaddada cewa, matakin da wasu ‘Yan kura-kurai Ke yi bai nuna kimar runduna ‘Yan sanda Najeriya ba.

Wannan dai ya zama karin haske ga shari’ar ‘yan sanda uku da ake tsare da su, dangane da mutuwar Abubakar Auwal, wanda ya mutu a hannunsu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bello M. Sani, ya bayar da umarnin a tsare su ne, inda inda ake zargin cewa , za a dauki matakin ladabtarwa kan lamari domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Jami’an rundunar ‘yan sandan reshen Jega sun kama Abubakar Auwal bisa zargin satar rigunan manyan motoci.

Jami’an sun yi ikirarin cewa ya fadi ne, a tsare kuma an garzaya da shi asibiti, inda ya mutu.

Sai dai CP din ya bayar da umarnin mika karar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID), inda aka samu jami’an uku da laifi tare da tsare su.

An gurfanar da jami’in ‘yan sandan Dibisional (DPO) mai kula da sashen Jega kuma an mika shi ba tare da bata lokaci ba.

Rundunar ‘yan sandan ta jaddada cewa, matakin da wasu ‘yan kura-kurai ke yi bai nuna kimar rundunar ‘yan sandan Nijeriya ba, don haka a kullum ana daukar matakan ladabtarwa da su domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.