Take a fresh look at your lifestyle.

Abokin Peter Obi, Obaze ya yi murabus daga jam’iyyar Labour

59

Mista Oseloka H. Obaze, babban aminin Mista Peter Obi, Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, ya yi murabus daga mukaminsa na jam’iyyar.

Obaze ya bayyana hakan ne, a wata wasika da ya aikewa shugaban kungiyar LP a Ochuche Ward 406, karamar hukumar Ogbaru a Awka a ranar Lahadi.

Obaze, tsohon jami’in diflomasiyya na Majalisar Dinkin Duniya ya kasance sakataren gwamnatin Anambra a karkashin Obi, kuma ya yi aiki kafada da kafada da shi a matsayin mai ba da shawara kuma jigo a jam’iyyar har sai da ya yi murabus daga LP.

Ya ce matakin da ya dauka shi ne, ya nuna rashin amincewarsa da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani na gwamna da jam’iyyar ta gudanar a Anambra ranar 5 ga watan Afrilu.

A cewarsa, bisa ga wannan wasika, na mika takardar murabus na daga jam’iyyar Labour (LP).

“Tsarin, aiki da sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar Labour da aka gudanar a ranar 5 ga Afrilu, 2025 a Awka, na cike da kura-kurai, zamba da aikata laifuka.

“Bai yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba, da kuma samar da muhimman dabi’u ko ka’idojin dimokradiyya.

“Saboda haka, daga yanzu na raba kaina daga Jam’iyyar Labour,” in ji shi.

Obaze ya shaida wa manema labarai cewa “wasikarsa gaskiya ce, kuma ya yi magana don kansa”.

Obaze ya kuma bayar da misali da rikicin shugabancin jam’iyyar LP, a matakin kasa da kuma yadda shugabannin jam’iyyar suka ki yin sulhu ko sasanta bangarorin Julius Abure da Sen. Nenadi Usman.

Sai dai bai bayyana yunkurinsa na gaba a siyasa ba.

Obaze ya yi murabus daga PDP a 2022, mako daya gaban Peter Obi, zuwa jam’iyyar Labour.

Daga nan ya zama manajan yakin neman zaben Peter Obi, kuma daya daga cikin fitattun da ke goyon bayan.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.