Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Juma’a ya gabatar da kudurin kasafin kudin shekarar 2023 na Naira tiriliyan 19.76 ga majalisun dokokin kasar biyu.
Kasafin kudin Naira Tiriliyan 19.76 wanda ya karu da kashi 15.37 cikin 100 daga adadin da aka ware a shekarar 2022 shi ne na karshe da Shugaba Buhari zai gabatar kafin wa’adinsa ya cika, kuma a
A cewar shugaban, wannan kasafi na 8 an yiwa lakabi da kasafin kudin dorewa da mika mulki.
Shugaba Buhari a lokacin da yake jawabi ga ‘yan majalisar ya ce kasafin kudin mika mulki na shekarar 2023 an tsara shi ne domin magance muhimman batutuwa da kuma kafa kwakkwarar harsashi ga gwamnati mai zuwa.
Ya bayyana cewa bisa la’akari da ma’auni da kuma hasashen kasafin kudi, ya kamata samar da kudaden shiga ya kai kusan Naira Tiriliyan 16.87.
Leave a Reply