Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar TETFUND Ya Yaba Da Aikin Daukar Ma’aikata A Kwara

81

Mamba mai wakiltar Arewa ta tsakiya a kwamitin amintattu na asusun tallafawa manyan makarantu (TETFund), Nurudeen Balogun ya yabawa gwamnatin jihar Kwara bisa kammala aikin daukar ma’aikata na Hukumar Koyarwa ta Jihar (TESCOM).

Daukar ma’aikata ta kunshi malamai 1,800, jami’an tsaro 200, da ma’aikatan da ba na koyarwa ba guda 100 .

Adeyemi, a cikin wata sanarwa, ya bayyana tsarin daukar ma’aikata a matsayin nasara mai cike da tarihi da kuma kyakkyawan misali na gaskiya, cancanta, da jajircewa wajen daukar ma’aikatan gwamnati.

“Wannan wani muhimmin ci gaba ne, ga jihar Kwara “Ina yaba wa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, bisa jagorancinsa na hangen nesa da kuma kiyaye ka’idojin da cancanta a cikin wannan gagarumin daukar ma’aikata.” Wakilin Hukumar ya bayyana hakan.

Ya kuma yaba wa Shugaban Hukumar TESCOM, Malam Bello Abubakar da duk masu ruwa da tsaki wajen gudanar da aikin cikin gaskiya da sanin yakamata.

Adeyemi ya bayyana cewa, hada da gwajin magunguna ga malamai, da nuna jajircewar jihar wajen samar da ingantaccen ilimi da kuma jin dadin dalibai.

“Wannan daukar ma’aikata ba wai a ma’auni ne kawai ba, tarihi ne, har ma da tsarin da ya gindaya don wasu su bi, nasara ce ga shugabanci na gari, nasara ce ga ilimi, kuma nasara ce ga jihar Kwara,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar ta dauka malamai 8000, daukar ma’aikata domin bunkasa koyarwa, tallafawa da ci gaban bil’adama a jihar.

“Wannan ya biyo bayan daukar malamai 4,700 da aka dauka a shekarar 2021 yayin da jimillar 22,953 suka nemi guraben aikin Hukumar Koyarwa da kuma 33,971 da aka sanya wa ma’aikatan ilimi na bai daya.”

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.