Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Manyan Sakatarorin Dindindin Guda 2.

234

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da manyan sakatarorin dindindin guda biyu a wani taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka fadada a Abuja, babban birnin Najeriya.

Takaitaccen an gudanar da shi ne, a kashi daya kuma Daraktan ofishin yada labarai na fadar shugaban kasa, Biodun Oladunjoye ne, ya shirya shi.

Sabbin sakatarorin dindindin guda biyu da aka rantsar sune: Mista Rafiu Olarinre Adeladan (Jihar Oyo) da Muktar Mohammed (Jihar Jigawa).

Shugaban ya kuma rantsar da shugaban hukumar yi wa masu yiwa kasa hidima, Savior Enyiekere da kwamishinoni 12.

A wani taron majalisar wakilai mai kashi biyu Shugaban Hukumar Hidima ta Majalisar Enyiekere da wasu mambobi goma sha biyu ( 12 ) sun yi rantsuwar kama aiki.

Enyiekere, kwararre kan muhalli, ya kasance mataimakin shugaban ma’aikata na shugaban majalisar dattawa kafin nadinsa, kuma zai yi aiki na tsawon shekaru biyar.

Sauran mambobin kwamitin guda goma sha biyu( 12 ) da aka zabo daga kowane shiyyoyin siyasa guda shida sune: Suleiman Othman Hunkuyi, Hon. Yusuf A. Yusuf Tabuka (Arewa maso Yamma) Aminu Ibrahim Malle Alhaji Lawan Maina Mahmud Arewa maso Gabas), Nnanna Uzor Kalu Festus Ifesinachi Odii (Kudu maso Gabas), Patrick A. Giwa, Mrs. Mary Ekpenyong (Kudu)

Membobin Hukumar za su rike mukaman na tsawon shekaru biyar.

Majalisar ta kuma yi shiru na minti daya don karrama tsohon karamin ministan harkokin waje, Dubem Onyia wanda ya rasu a ranar 10 ga Maris, 2025.

Wadanda suka halarci taron takaitaccen rantsuwar sun hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu.

 Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki Wale Edun, da takwaransa na Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Tattalin Arziki Atiku Bagudu da Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Kasa, Mohammed Idris da sauran mambobin majalisar zartarwa.

Idan za a iya tunawa, zaman majalisar zartarwa na karshe da aka yi a ranar 3 ga watan Maris, lokacin da gwamnatin tarayya ta amince da Naira biliyan 2.5 don siyan tauraron dan adam na sa ido wanda aka fi sani da tsarin samar da mafita, don yaki da ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a fadin kasar nan.

A yayin taron Majalisar na Maris, gwamnatin ta kuma amince da shirin inshorar ₦1.09 ga muhimman kadarori da ma’aikata a duk filayen jiragen sama na tarayyar Najeriya

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.