An dai gano gawarwakin ‘yan jaridar kasar Afirka ta Kudu Sibusiso Aserie Ndlovu da takwararsa Zodwa Precious Mdhluli a lardin Limpopo fiye da watanni biyu.
An gano gawarwakin ne a wani daji mai nisa kuma suna cikin wani yanayi na rubewa.
Yayin da ake ci gaba da jiran tabbatar da DNA kungiyoyin yada labarai sun ce tuni kungiyoyin bincike sun gano gawarwakin.
‘Yan sanda sun cafke mutane biyar da ake zargi da hannu a lamarin.
Rahotanni sun ce hukumomi sun kwato kayayyakin da aka sace da suka hada da kayan daki Da na’urori da kuma sassan motar da ke da alaka da ma’auratan.
Ndlovu wanda ya kafa gidan rediyon Capital Live da ke Pretoria ya bace tare da Mdhluli tun ranar 18 ga Fabrairu.
Mutuwar nasu dai ya sa al’ummar kafafen yada labarai su tada jijiyoyin wuya.
“Na yi matukar bakin ciki. Mun kasance da bege… Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalai,” in ji Elijah Mhlanga shugaban dandalin yada labarai da sadarwa na Afirka.
Lamarin ya nuna yadda Afirka ta Kudu ke fama da tashe-tashen hankula.
Kasar ta sami kisa sama da 26000 a cikin 2024 matsakaita na kashe-kashe 72 a kowace rana.
Africanews/Aisha.Yahaya, Lagos