Gwamnatin kasar Sin ta yi nadamar lamarin da ya kai ga janyewar ‘yan wasan Najeriya daga halartar gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da Guangzhou wanda aka shirya gudanarwa a kasar Sin daga ranar 10 zuwa 11 ga watan Mayun 2025.
Har ila yau kasar Sin ta jaddada aniyar ci gaba da ba da tallafi ko mu’amala a fannoni daban daban ciki har da wasanni. Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani ga rahoton da hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Najeriya (AFN) ta fitar inda ta sanar da janyewarta daga gasar sakamakon tsaikon da hukumomin kasar Sin suka yi na biza. Ofishin jakadancin China a Najeriya ne ya bayyana hakan.
A cewar sanarwar rahoton da AFN ta fitar bai dace da gaskiyar lamarin ba. Sanarwar ta kara da cewa ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya na son bayyana gaskiya da matsaya kamar haka:
“A ranar 24 ga Afrilu ofishin jakadancin ya karbi wasika daga hukumar wasanni ta kasa (mai kwanan wata 22 ga Afrilu) inda ta bukaci a taimaka wajen sarrafa biza ga ‘yan wasan Najeriya don halartar bikin wassani a kasar Sin ” in ji ofishin jakadancin Sin.
“Nan da nan ofishin jakadanci ya yi magana da hukumar tare da jagorance da don shirya kayan da suka dace don hanzarta neman biza. A ranar 6 ga Mayu Cibiyar Bukatar Visa ta kasar Sin ta karbi kayan aikin da ‘yan wasan Najeriya suka gabatar.”
Kara karanta: Jinkirin Biza: Najeriya ta janye daga wassani duniya a China
Sanarwar ta kuma bayyana cewa nan take ofishin jakadanci ya fara aikin cikin gaggawa tare da bayar da cikakken taimako ga masu neman Najeriya tare da kammala bayar da bizar a ranar 8 ga watan Mayu.
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya yana ba da goyon baya ga hadin gwiwa tsakanin jama’a da wasanni a tsakanin kasashen biyu yana mai bayyana maraba ga ‘yan wasan Najeriya da su halarci bikin a kasar Sin tare da taimakawa kan neman biza cikin inganci da kwarewa.”
“Ya kamata a lura da cewa bayar da bizar wani lamari ne da ya shafi ikon mallakar kasa kuma dukkanin ofisoshin jakadancin kasashen waje suna buƙatar masu neman su samar da takaddun da kayan aiki tare da ba da isasshen lokaci don aiwatar da aikace-aikacen.”
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya ya bayyana cewa yana nan a shirye don inganta mu’amalar sada zumunta tsakanin jama’ar Sin da Najeriya Kuma za ci gaba da ba da tallafi da taimako don yin mu’amala da hadin gwiwa a fannoni daban daban ciki har da wasanni
Aisha.Yahaya, Lagos