Jam’iyyar PDP a Jihar Legas ta sanya ranar Asabar mai zuwa Don zaben fidda gwani na ‘yan takarar da za su fafata a zaben kananan hukumomin Jihar da za a yi ranar 12 ga watan Yuli.
A wata hira da mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Mista Hakeem Olalemi ya ce za a gudanar da zaben fidda gwani a kananan hukumomi daban-daban kuma ’yan takara za su fito ta hanyar amincewa.
“Jam’iyyar mu PDP za ta gudanar da zabukan fitar da gwani na kananan hukumomi a Jihar Legas a sakatarorin kananan hukumomin jam’iyyar a ranar Asabar 17 ga watan Mayu.
“‘Yan takarar shugaban kasa da kansiloli za su fito ta hanyar yarjejeniya,” in ji jigon na PDP.
A cewar sa jam’iyyar PDP na shiga zaben kansiloli domin samun nasara . “Muna da tabbacin cewa damarmu za ta yi haske sosai a zaben kananan hukumomi na gaba. “Mun san cewa jam’iyya mai mulki ita ce hukumar zabe ta Jiha amma za mu kasance a filin tare da jam’iyyar APC mu hada kai da su.
Ya kara da cewa “Da yardar Allah za mu yi nasara a shirye muke don zaben a zahiri da dabi’a da sauran su.”
A wata zantawa ta dabanb shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Legas Mista Phillips Aivoji ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta yi kyau a zaben.
“Muna taka rawa ne domin mu samu nasara za mu ci gaba da yin gangamin neman goyon bayan jama’a mu zabi PDP.
“Na yi imanin cewa damar PDP na da haske a wasu yankunan yayin da za mu yi watsi da ita a wasu majalisa ” in ji Aivoji. Ya ce mazauna Jihar za su shaida ’yanci kuma za su ji dadin jagoranci da
shirye-shirye masu son jama’a idan suka zabi PDP ta yi mulki a kananan hukumomi daban-daban.
“Mutanen Legas sun tsaya tsayin daka a jam’iyyar PDP sun tsaya don samun kyakkyawan shugabanci.
Shugaban ya kara da cewa “Sun tsaya don samun gwamnati mai ma’ana da mutane za su kasance na daya a duk abin da muke yi idan aka zabe PDP.”
Aisha.Yahaya, Lagos