Ministocin harkokin wajen Turkiyya da Amurka da Siriya za su gana a kudancin Turkiyya a yau Alhamis domin tattaunawa kan alkawarin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na dage takunkumin da aka kakabawa Siriya a kwanakin baya Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan ya tabbatar a ranar Larabda ta gabata.
A ranar Talata ne Trump ya sanar da dage takunkumin da aka kakaba bisa bukatar Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman da kuma shugaban kasar Turkiyya Tayyip Erdogan.
Matakin ya nuna gagarumin sauyi a manufofin Amurka gabanin ganawar da Trump zai yi a ranar Laraba da shugaban masu kishin Islama na Syria Ahmed al-Sharaa da yarima mai jiran gado na Saudiyya da kuma Erdogan wadanda suka halarci kusan.
Dage takunkumin ya kasance wata muhimmiyar manufa ga Riyadh da Ankara wadanda suka fito a matsayin manyan masu goyon bayan sabon shugabancin Syria tun bayan hambarar da Bashar al-Assad a watan Disamba da ta gabata wanda ya kawo karshen yakin basasa na shekaru 14.
Da yake magana da TRT Haber gabanin taron ministocin harkokin wajen NATO na yau da kullum a Antalya Fidan ya kira taron shugabannin a ranar Laraba da ta gabata a matsayin mai tarihi yana mai cewa sassauta takunkumin zai bude muhimman hanyoyin hada-hadar kudi da zuba jari da samar da ababen more rayuwa ga tattalin arzikin Syria da yakin.
“Gobe mu uku ne Sakatare Rubio da Minista al-Shibani da ni za mu gana bayan zaman NATO don yin aiki Inda aka aiwatar da cikakkun bayanai game da yarjejeniyar da shugabanninmu da suka tsara” in ji Fidan yayin da yake magana da Sakataren Harkokin Wajen Amurka da Marco Rubio da Ministan Harkokin Wajen Syria Asaad al-Shibani.
Ya yarda cewa akwai cikas na doka da na gudanarwa a Amurka amma ya jaddada aniyar Trump na ci gaba.
Ya kara da cewa “Tare da kudurin shugaban kasa da kuma aikin da za mu yi muna fatan ganin an dage wadannan takunkumi nan ba da jimawa ba.”
Dage takunkumin da Amurka ta kakaba mata zai sake hade kasar Siriya da tsarin hada-hadar kudi na duniya wanda zai iya kara kaimi ga ayyukan agajin jin kai da saka hannun jarin kasashen waje da kasuwanci yayin da kasar ta fara aikin na sake gina kasar.
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos