Majalisar dattawan Najeriya sun tabbatar da nadin kwamishinonin zabe biyar RECs na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Tabbacin nasu ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin kan INEC a zauren majalisa ranar Laraba da ta gabata.
Shugaban kwamitin Sanata Simon Lalong (APC-Plateau) ne ya gabatar da rahoton.
INEC Ta Gabatar Da Muhimman Shawarwari Takwas Na Gyaran Zabe Ga ‘Yan Majalisu
RECs da aka tabbatar sun hada da: Umar Garba da mai wakiltar Kano da Sa’ad Idris (Bauchi) da Chukwemeka Ibeziako (Anambra) da Umar Mukhtar (Borno) da Dr Johnson Sinkiem (Bayelsa).
Lalong a cikin jawabinsa ya ce kwamitin ya yi la’akari da ci gaba da kwarewar aikisu da kuma cancanta su da aka zaba yayin tantance su.
Ya ce wadanda aka nada sun amsa tambayoyi cikin nasara inda ya bayyana cewa dukkansu sun cancanci nadin.
“Bayan yin nazari a hankali a kan dukkan takardunsu da suka dace na wadanda aka zaba tare da yin la’akari da matakan da suka dace da kwarewa da cancanta da kuma amincin su wannan kwamiti na ba da shawarar cewa majalisar dattawa ta tabbatar da wadanda aka zaba,” in ji shi.
NAN/Aisha