Gwamnatin Jihar Oyo ta shirya taron horas da kansilolin kananan hukumomi 453 da mataimaka na musamman 420 a fadin kananan hukumomin Jihar 33.
Taron wanda aka gudanar a garin Ibadan babban birnin Jihar ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin masarautu ta shirya shi domin baiwa masu kulawa da mataimaka na musamman kwarewa da ilimi domin inganta harkokin mulki a matakin farko.
Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu Ademola Ojo ya jaddada a wurin horon cewa taron bitar na samar da ayyukan yi a matakin farko inda ya bukaci mahalarta taron su tashi tsaye wajen amfani da ilimin da suka samu.
Ojo wanda ya samu wakilcin Darakta mai kula da ma’aikatar Mista Oladotun Olamide ya yabawa kokarin gwamnati mai ci a karkashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde bisa jajircewar da take yi na samar da shugabanci na gari a dukkan lungu da sako na Jihar.
Da take gabatar da laccar shugaban mai ba da shawara daga sashen nazarin tattalin arzikin noma na jami’ar Ibadan Farfesa Kemisola Adenegan ya horas da mahalarta taron kan ilimin da suka dace da kwarewa da suke bukata don tallafawa gudanar da al’amuran kananan hukumomi masu inganci.
Ta kuma ja hankalin mahalarta taron da su kasance masu himma wajen yanke shawara da tafiyar da harkokin mulki a mazabunsu.
Da yake jawabi a madadin mahalarta taron kansilan mai kula da harkokin matasa da wasanni na karamar hukumar Iseyin Hammed Adebisi ya yaba da shirin inda ya bayyana cewa zai sake fasalin tsarin tafiyar da shugabanni a matakin kananan hukumomi wajen magance matsaloli da ci gaban kasa.
Ya yi kira ga ma’aikatar da ta shirya karin tarurrukan horaswa inda ya jaddada bukatar karfafawa ma’aikatan kananan hukumomi karfi domin samun ingantaccen shugabanci da ci gaban mutane.
Aisha.Yahaya, Lagos