Take a fresh look at your lifestyle.

Khamenei A Iran Ya Yi Allah Wadai Da Bukatar Amurka Da Ba A Saba Gani Ba A Tattaunawar Nukiliyar

33

Jagoran juyin halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce bukatun Amurka na cewa Tehran ta guji inganta makamashin Uranium “ya wuce gona da iri” in ji kafofin yada labaran kasar yana mai bayyana shakku kan ko tattaunawar nukiliya za ta kai ga cimma yarjejeniya.

Ba na tsammanin tattaunawar nukiliya da Amurka za ta haifar da sakamako. Ban san abin da zai faru ba,” in ji Khamenei ya kara da cewa ya kamata Washington ta guji yin mummunar bukatu a cikin shawarwarin.

Duk da hasashen da ake yi na cewa za a gudanar da shawarwari karo na biyar a karshen mako a birnin Rome tattaunawar nukiliyar ta yi tsami yayin da kasashen Iran da Amurka suka yi takun-saka kan batun inganta makamashin nukiliya.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Majid Takht-Ravanchi ya fada a ranar Litinin din da ta gabata cewa tattaunawar ba za ta yi nasara ba idan Washington ta nace cewa Tehran ta kaurace wa tace sinadarin Uranium a cikin gida wanda Amurka ta ce wata hanya ce ta kera bama-baman nukiliya.

Tehran ta ce shirinta na makamashin nukiliya yana da manufar zaman lafiya gaba daya.

Tun da farko a ranar Talata wani mataimakin ministan harkokin wajen Iran Kazem Gharibabadi ya ce Tehran ta karba kuma tana nazarin shawarar Amurka.

A makon da ya gabata Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Tehran na bukatar “ta yi sauri ko kuma wani abu mara kyau zai faru.”

Shugaban na Amurka ya sha gargadin Iran cewa za a kai mata harin bama-bamai tare da kakaba mata takunkumi mai tsanani idan har ba ta kai ga cimma matsaya ba wajen warware shirinta na nukiliya da ake takaddama a kai.

Trump wanda ya sanya yarjejeniyar 2015 mai zaman kanta a cikin goyon bayan Iran shi ma ya sake kakaba takunkumin Amurka kan Iran.Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta mayar da martani da kara habaka.

 

 

 

Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.