Ministan yada labaran Najeriya Mohammed Idris ya bayyana yabo ga gwamnan jihar Kaduna Uba Sani dangane da kokarin da ya yi na sake kafa ma’aikatar yada labaran jihar Kaduna.
Wannan muhimmiyar shawara wacce ya faru bayan shekaru goma da rugujewar ta ya yi daidai da ƙarar da Ministan ya yi yayin taron Majalisar Watsa Labarai ta Ƙasa (NCI) na Disamba 2024.
A yayin wannan taro an karfafa wa jihohi gwiwa da su ba da fifiko wajen farfado da ko kafa ma’aikatun yada labarai don inganta harkokin mulki da cudanya da jama’a da samar da hadin kan kasa.
Ministan ya amince da matakin da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da hadafin gudanar da mulki na gaskiya da kuma sadarwa tsakanin ‘yan kasa a fadin Najeriya.
Ya kara da cewa ta hanyar maido da ma’aikatar jihar Kaduna ta nuna kudurinta na ganin gwamnatin tarayya ta samar da tsarin da bayanai da suka dace inda jihohi da na tarayya ke hada kai don kara habaka labaran ci gaba da dakile labaran karya da inganta hadin kan kasa.
A cewar Ministan: “Farfado da Ma’aikatar Yada Labaran ta Kaduna zai inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomin yada labaran na tarayya da na Jihohi tare da ba da damar yin aiki tare a kan abubuwan da suka sa a gaba na kasa kamar tsaro da kiwon lafiya da ilimi da sake fasalin tattalin arziki.”
Ya bayyana cewa tare da ma’aikatar jiha mai aiki, ‘yan ƙasa a Kaduna za su sami ingantacciyar hanyar samun ingantattun bayanai kan manufofin gwamnati da shirye-shirye da dama da haɓaka haɗa kai da gudanar da mulki.
Ministan ya kara da cewa “zai yi aiki a matsayin kariya ta gaba daga labaran karya da kalaman raba kan jama’a da kiyaye amanar jama’a ta hanyar sadarwar kan lokaci da daidaito da kuma al’adu.”
Ministan yada labaran kasar ya nanata kira ga daukanin jihohin da ba su da ma’aikatun yada labarai na aiki da su yi koyi da Kaduna domin irin wadannan cibiyoyi na da matukar muhimmanci wajen dinke barakar sadarwa da samar da rikon amana da kuma tabbatar da cewa babu wani dan Najeriya da aka bari a baya wajen neman ci gaba mai dorewa.
Aisha. Yahaya, Lagos