Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta Ja Kunnen ‘Yan Siyasa Su Zama Masu Bin Doka Da Oda
TIJJANI USMAN BELLO
Bubban Sufeto Janar na ‘Yan Sandan, Usman Alkali Baba, ya yi wannan horonne a lokacin da yake kaddamar da katafaren Ofishin shiyya na Cajis Ofis a garin Benishek hedikwatar karamar hukumar Kaga dake jihar Borno, a wata ziyarar aikin kwanaki 2 da ya kawo jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya.
Usman Alkali Baba, ya ci gaba da cewa” Wajibine ‘Yan siyasa su mutunta dokar zabe ta shekara 2023 ta yadda zasu gudanar da yakin neman zabensu cikin lumana da kwanciyar hankali.
” Mu jami’an tsaro muna nan muna gudanar da shirye-shiryen gudanar da zaben ta wajen samar da kayayyakin aiki tare da gudanar da horar da jami’anmu da nufin a sami daman gudanar da zaben shekara ta 2023, cikin kwanciyar hankali da lumana.”
Sufeto Janar din ya kuma ce sun dauki kuratan jami’an’yan sanda dubu 10, a kwanannan kuma aka turasu jihohin da suka fito, don taimakawa jami’ansu Domin inganta aiyyukan ‘yan sanda a tsakanin alumma, da nufin dakile aikata munanan Laifuka a kasa baki daya.
Tun da farko a jawabinsa na maraba, kwamishinan ‘yan sandan jihar Barno Malam Abdu Umar, ya fadi irin asarorin da rundursa ta yi a cikin shekararu 11, sakamakon Hare-haren Kungiyar Boko Haram, in da ya ke cewa“A kalla mun rasa jami’anmu har guda dari 389, a ya yin da 450 suka ji munanan raunuka Barikoki 24 ne suka kone, a ya yinda suka kone mana Cajis Ofis 30, a a cikin garin Maiduguri da wasu yankunan kanan hukumomin da yakin ya shafa,”
Shiko gwamnan jihar Bornon Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bukaci ci gaba da samun cikakken hadin kaine a tsakanin jami’an tsaro, ya ce “Idan hakan ya dore to babu ko shakka za’a ci nasarar abin da aka sanya a gaba na yakar ayyukan ta’addaci a kasa baki daya.”
Baya ga kaddamar bude katafaren Ofishin shiyya mai dauke da saman bene har hawa 3, makare da kayayyakin aiki irin na Zamani, Sufeto Janar din ya kuma bude wasu sabbin dama wadanda aka gyara na Ofisoshi da Barikoki dama Kolejin ‘Yan Sandan da ‘Yan ta’addan Boko Haram suka lalata.
Excellent content! You’ve made some excellent
observations. Keep up the good work
Interesting post! This is very insightful. Will share
this with others