Uwargidan shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu ta gana da wacce ta kafa gidauniyar Qatar Sheikha Moza bint Nasser Al-Missned domin neman goyon bayan kungiyar tare da kawo dauki ga yara sama da miliyan 15 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.
Misis Tinubu ta ce gwamnatin Najeriya ta hannun ma’aikatar ilimi, ta shirya aiwatar da wani tsari na sauya tsarin makarantun Almajiri wanda ya hada ilimin addinin Musulunci da na boko.
Ta ce; “Wadannan Makarantu za su dauki nauyin kula da yaran a cikin ingantaccen yanayi na koyo, wanda zai hada da masallacin ibada hada sana’o’i da samar da wuraren kwana ga dalibai da kuma wurin zama ga Limamai da masu kula da su.
“Wannan cikakkiyar dabarar za ta ba yara damar samun ilimi na yau da kullun da na Musulunci ba tare da amfani da su ba tare da samar musu da dabarun rayuwa wanda zai ba su damar gina rayuwarsu da kuma ba da gudummawa mai ma’ana ga al’umma.”
Sai dai uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa kasar na bukatar tallafi da taimakon kasashen waje domin cimma burin da aka sa gaba. “Duk da haka idan aka yi la’akari da girman wannan kalubale da kuma bukatu da ake da su a kan albarkatun kasa Najeriya ba za ta iya cimma wannan ita kadai ba muna bukatar abokan huldar kirkire-kirkire kuma mai martaba ta wakilci daidai irin abokan hangen nesa da za su taimaka mana mu tabbatar da wannan mafarkin,” in ji mai masaukin nata.
Misis Tinubu ta yabawa Sheika Moza bisa irin gudunmawar da ta yi musamman a fannin ilimi ta gidauniyar da ta gina birnin ilimi na Qatar da sama da makarantu 40 da suka hada da Jami’o’i da kuma dakin karatu na kasar Qatar.
“Ina alfahari da sanin nasarorin da kuka samu wajen zarce manufar shigar da yara marasa galihu miliyan 10 zuwa makaranta, da duk abin da kuke ci gaba da yi ga bil’adama a duniya.
Uwargidan shugaban Najeriyar ta ce “Kallon ku kuna yin wadannan manyan ayyuka ya kara tabbatar mana da cewa sauyi mai yiwuwa ne kuma na yi imanin tuntubar kungiyar ku mai kima zai iya ba da tallafin da muke bukata cikin gaggawa,” in ji uwargidan shugaban Najeriya.
Taimako
A nata martanin shugabar gidauniyar Qatar Sheika Moza Bint Nasser Al-Missned ta yi alkawarin bayar da gudunmowar bayar da tallafin karatu ga Almajirai da ‘ya’yan da ba su zuwa makaranta a Najeriya.
Ta bayyana cewa gidauniyar za ta yi aiki tare da ma’aikatar ilimi ta wannan fanni da kuma horar da ma’aikata da malamai a makarantun idan aka kafa su don tabbatar da kyakkyawan sakamako.
Tun da farko Mrs Tinubu ta ziyarci hedkwatar gidauniyar Qatar inda shugaban gidauniyar Yousif Al Na’am da sauran su suka suka zagaye da ita.
An shaida mata cewa Najeriya na da tsofaffin dalibai 41 daga Jami’ar Muhammad Khalifa.
Uwargidan shugaban kasar ta ziyarci kasar Qatar ne tare da ministan lafiya da walwalar jama’a Farfesa Muhammad Pate da karamar ministar ilimi Farfesa Suwaiba Ahmed da kuma babban sakataren hukumar Almajiri da ilimin yaran da ba sa zuwa makaranta Dr Muhammad Sani Idris.