Take a fresh look at your lifestyle.

Hare-Haren Jiragen Saman Rasha Sun Kashe Mutane 3 Tare Da Raunata 29 A Kyiv

41

Hukumomi sun ce Rasha ta kai hari kan babban birnin Ukraine Kyiv da jirage marasa matuka, inda suka kashe mutane uku a gidajensu tare da raunata 29.

Daga cikin mutane 29 da suka jikkata, bakwai kananan yara ne, a karo na biyu a jere da aka kai hari da dare a birnin Kyiv, domin lakume rayukan fararen hula. Ministan cikin gida na Ukraine Ihor Klymenko, ya ce wata mace mai shekaru 19 da mahaifiyarta mai shekaru 46 na daga cikin wadanda aka kashe.

Jiragen saman Rashan sun kuma haddasa gobara a wasu gine-gine biyu a gundumar Desniyaski babban birnin kasar.Jami’an agajin gaggawa sun kwashe fararen hula daga wani bene mai hawa tara da wani bene mai hawa 16, inda suka kashe wuta tare da kwashe baraguzan ginin.

Olha Yevhenivha, mai shekaru 74, mazaunin Kyiv ta ce akwai hayaki mai yawa daga gobarar da ta sa ba za ta iya barin gidanta ba.

“Ko da har ya zuwa yanzu tagogin mu gaba ɗaya baƙar fata ne daga hayaƙi, kuma ba zai yiwu a sauka ba, shi ya sa muka sanya rigar barguna a kan kofofinmu da baranda,” in ji ta.

Rasha ta kai wa Ukraine hari da jirage marasa matuka 101 cikin dare zuwa ranar Lahadi, a cewar rundunar sojin saman Ukraine, inda aka harbo 90 daga cikinsu tare da kawar da su. Sanarwar ta ce Jiragen marasa matuka guda biyar sun kai hari a wurare hudu sannan tarkacen jirgin ya fado a wasu wurare biyar.

Harin ya zo ne kwana guda bayan da makamai masu linzami da jiragen saman Rasha suka kashe mutane hudu, ciki har da biyu a Kyiv, wanda ya haifar da sabon roko daga shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy kan tsarin tsaron sararin samaniyar kasashen yamma.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta yi ikirarin a ranar Lahadin da ta gabata cewa, a ranar Lahadin da ta gabata, dakarunta sun kai farmaki kan wuraren samar da makamashi da kayayyakin aikin jiragen kasa da ke hidima ga yakin Ukraine, da kuma wasu hare-haren soji kamar wuraren tura sojoji da masana’antar sarrafa jiragen sama.

Sai dai ba ta yi tsokaci ba musamman kan hare-haren da aka kai a Kyiv, da kuma asarar fararen hula da Ukraine ta bayar.

A yankin Bryansk na Rasha da ke kusa da Ukraine, an kwantar da fararen hula biyu a asibiti sakamakon hare-haren da jiragen saman Ukraine suka kai, a cewar gwamnan yankin Alexander Bogomaz. Akalla jirage marasa matuka na Ukraine 26 ne aka harbo a yankin kudu maso yammacin kasar Rasha a ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda ma’aikatar tsaro a birnin Moscow ta sanar.

AP/Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.