Take a fresh look at your lifestyle.

Najeriya Ta Yabawa Kasashen Duniya Wajen Nuna Goyon Baya Kan Hakuri Da Addini

8

Gwamnatin Najeriya ta yabawa kasashen duniya kan yadda suka nuna goyon bayansu ga Najeriya biyo bayan kalaman da tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kan rashin yarda da addini a kasar.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ne ya yi wannan yabon a Abuja a lokacin shirye-shiryen bikin cikar jamhuriyar Angola shekaru 50 da samun ‘yancin kai.

Mista Idris ya bayyana kalaman na Amurka a matsayin abin takaici ganin yadda wasu ke son sauya salon labari ga ‘yan Najeriya a matsayin kasa.

Ya yi bayanin cewa “Najeriya na yin duk mai yiwuwa don warware kuskuren da gwamnatin Amurka ta yi ta hanyoyin diflomasiyya.”

A cewarsa, yana samun sabbin bayanai da ke fitowa daga Amurka kan wannan batu.

Don haka Ministan ya yi kira ga daukani ‘yan kasar da su hada kai su domin yakar duk wani abu da zai zubar da kimar kasarmu Najeriya.

“Wannan ba lokacin siyasa ba ne, wannan ba lokaci ba ne da za a ce kuna so ku yi imani ko ba ku yi ba, wannan shine lokacin da za ku yi tunani da kuma nuna halin Dan Najeriya,” in ji shi.

Mista Idris ya ci gaba da cewa Najeriya na da kalubalen tsaro amma a siffanta Najeriya a matsayin kasar da ba ta amince da ’yancin addini ba daidai ba ne, marar tushe ba tare da gaskiya ba kuma cike da karya.

A nasa jawabin, jakadan, mai cikakken iko, Jamhuriyar Angola a Najeriya, Jamhuriyar Benin, Jamhuriyar Nijar da kuma kungiyar ECOWAS, Jose Zau ya yaba wa Najeriya bisa daukar kwararan matakai na tabbatar da aniyar Angola ta samu ‘yanci kai da zaman lafiya a kasar.

Malam Zau ya ce; “Shugabannin Najeriya da ‘yan kasar sun ba da gudunmawa sosai wajen ganin Angola ta samu ‘yancin kai a shekarar 1975”.

Jakadan kasar Angola mai cikakken iko ya jinjinawa tsohon shugaban kasa, Marigayi Janar Murtala Mohammed, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Janar Ike Nwachukwu mai ritaya, tsohon kwamanda, babban hafsan soji na Majalisar Dinkin Duniya a Angola, Manjo Janar Chris Garba mai ritaya da sauran da dama wadanda suka bayar da gudunmawa mai tsoka.

Dukkansu sun samu lambar yabo ta ofishin jakadancin Angola da ke Najeriya ya ba su.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris wanda ya mika allunan ga dukkan wadanda suka samu kyautar ya kuma samu lambar yabo ta musamman daga kasar Angola daga bisa jajircewar da bayar da gudunmawar da yake baiwa kasar Angola.

A yayin da ake ci gaba da gudanar da taron a Abuja, Najeriya, Angola kuma tana karbar bakuncin wasu fitattun ‘yan Najeriya wadanda ta wata hanya ko kuma wata hanya ta ba da gudummawar ‘yancin kai shekaru 50 da suka gabata a Luanda, babban birnin kasar.

Wadannan fitattun ‘yan Najeriya sun samu karramawar kasa a kasar Angola.

Sun hada da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo; Marigayi shugaban kasa Muritala Mohammed da Farfesa Ibrahim Gambari wanda ya karbi lambar yabon da kansa yayin da wasu ke karbar ta hannun wasu daga cikin iyalansu.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.